Da yammacin Litinin da ta gabata, mai dakin Gwamnan Jahar Kebbi kuma Khadimatuddeen Dr. Zainab Shinkafi Bagudu tare da rakkiyar yanuwa da mashwarta, ta samu kai ziyara ga uwa mabada mama wato Hajia Koli Musa Yaro domin ganin lafiyar ta. Ta samu tarbo daga matan Alhaji Faruk PA wato Haj Rashida, Haj Asmau da kuma Haj Maryam.
Hajia Koli wadda take mahaifiya ga Alhaji Faruk Musa Yaro PA ga mai girma Gwamna, ta nuna mutukar farin cikinta da wannan ziyarar ta HE Dr Zainab wadda ke matsayin diya a gareta tare da yimata adduar samun gamawa lafiya.
Daga nan ta zarce zuwa gidan Khalifa Muktar don jajantawa kan ibtila’in gobarar da ta afka masu wadda tayi sanadiyar rasa yaronshi mai shekaru 11 a duniya, tare da fatar Allah ya mayar masu da Alheri yajiqan magabata.
A haka kuma, Matar gwannna ta je taazia ga iyalen Dr Abubakar Dakingari baban Likita mai kuka da VVF da Government house wanda Allah Ya ma rasuwa. Ta iske mahaifiyar shi da matan shi kuma ta yi bayanin Irin gudumwar sa a jihar Kebbi tare da fatar Allah SWA Ya karbi bakuncin shi.
Haka zalika tayi zagayen sanbarka a gidajen angwaye Ibrahim Attahiru Alqali da Amaryarsa Hauwau Shehu Wala, sai Sanusi Bello Kalgo da amaryarsa Khadija Aminu S Gobir, tare da fatar Allah ya basu zaman lfy Amin.
Asmau Jafar Umar
SSA
16/02/2021