Ko mi yai zafi? Matashi ya kashe kansa ta hanyar caccaka wa al’aurarsa wuka a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi Mustapha Muhammad mazaunin unguwar Kurna layin Malam Na Andi, da ake zargin ya kashe kansa da kwalba.
Rudunar ƴan sandan ta ce matashin ya yi hakan ne bayan ya kulle kansa a wani gida da ke unguwar Masukwani a birnin Kano, ta hanyar hawa kan gilashin tagar ɗakin gidan ya kulle kansa.
Kakakin rundunar ƴan sandan Kano DSP Haruna Kiyawa ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, 14 ga watan Fabrairun da muke ciki, bayan samun rahoton cewar matashin ya shiga wani gida a unguwar Musukwani ɗauke da wata fasasshiyar kwalba a hannunsa.
DSP Kiyawa ya ƙara da cewa daga nan sai ya shiga wani ɗaki a gidan ya kuma yanke al’aurarsa da cakawa kansa kwalbar a wurare da dama a jikinsa.
“Jim kaɗan da samun wannan labari ne sai ƴan sanda muka je wannan gida aka ɗauke shi da gaggawa aka kai shi Asibitin Murtala da ke cikin gari, inda ba jimawa likita ya tabbatar da mutuwarsa a yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa,” in ji DSP Kiyawa.
BBC ta ji ta bakin ɗaya daga cikin matan gidan da ya shiga ya aikata hakan inda ta ce: “Mun tashi da safe muna aiki sai kawai muka ga wannan yaro ya shigo da gudu, bai zarce ko ina ba sai ɗakin mahaifiyata. Sai yake ta bige-bige yana fasa gilasai, muka yi muka yi ya buɗe ya ƙi. Sai aka fasa ƙofar.
“Anan ne fa aka ga ya jijjiwa jikinsa ciwo ya yanke gabansa, jini duk ya ɓata jikinsa.