Gwamna Bala Mohammed Ya Bada Umarnin Rushe Wani Gida Bayan An Samu Bindigogi Da Harsashai Sama Da Dubu Daya A Cikinsa
Gidan yana gundumar Majidadi (B) dake Unguwan Mahaukata a cikin garin Bauchi.
A yayin binciken, an gano cewar mai kula da ikon gidan mace ce. Kuma bayanai na gwada cewar mazauna gidan ko wadanda suke haya a gidan duk ana kan bincikar su yanzu haka, inda shi kuma gidan an bada umarnin rushewa ne domin ya zama izina ga ‘yan baya, don kada a rika bada mafaka ga muggan iri.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Bauchi Dr. Ladan Salihu shi ya Jagoranci tawagar don rushe gidan a nadadin Gwamna Sanata Bala Mohammed. Inda a jawabinsa ya ja hankalin jama’ar gari da su rika lura da bakin ido da shiga da fitar jama’a.
Ya ce “a kai rahoton duk wani bakon idon da aka gani ba a gane masa ba, domin ba za mu bari wani bata gari ya zo Bauchi ya samu mafaka ba saboda Bauchi jihar zaman lafiya ce”.
Allah kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Bauchi da Nijeriya baki daya. Amin Ya Allah.
Daga Maidarasu Misau