Magu Ya Taya Sabon Shugaba Murna
Sabon Shugaban Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa yace tsohon Shugaban Hukumar Ibrahim Magu ya kira shi ta waya da aka ba shi wannan mukami inda ya taya shi murna tare da yi mishi fatan alheri.
Abdulrasheed Bawa ya ƙara da cewa akwai dangantaka ta mutunci da girmamawa tsakaninsa da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu, wadda ba zata misaltu ba.
Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne yayin amsa tambayoyi a gaban Majalisar Dattawa lokacin tantance shi a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa.
Sabon Shugaban Hukumar ya bayyana yadda Magu ya kira shi a waya, ya taya shi murna a lokacin da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban hukumar.
“Ina da alaka mai kyau da tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Ya kira ni da aka zabe ni, ya yi mani fatan Ubangiji ya ba ni sa’a.” inji Abdulrasheed Bawa.
‘Yan Majalisar sun yi wa Bawa tambayoyi a game da yadda ake ruruta labaran ‘yan siyasar da ake bincike da zargin satar kudin al’umma, da zargin mayar da wasu ‘yan mowa wasu kuwa ‘yan bora da Hukumar ke yi.
Yan Majalisar sun yi wa Bawa tambayoyi a game da yadda ake ruruta labaran ‘yan siyasar da ake bincike da zargin satar kudin al’umma, da zargin mayar da wasu ‘yan mowa wasu kuwa ‘yan bora da Hukumar ke yi.
Abdulrasheed Bawa ya ce EFCC sun yi nasara a fiye da 90% na karar da ta shigar a kotu. Sannan ya kara da cewa EFCC ta yi nasarar daure ‘yan damfara duk da yawan bata lokacin da aka yi ana tataburza.
Bawa ya yi aiki a karkashin Magu wanda ya kasance mai gidansa a EFCC tsakanin 2016 da 2020. Har ana rade-radin an taba samun sa da aikata ba daidai ba a lokacin.
A tsakiyar shekarar bara ne aka dakatar da Ibrahim Magu daga aiki, sannan aka kuma nada wani kwamiti na musamman da ya yi bincike a kan ayyukan da ya yi a EFCC.
A ranar Laraba 24 ga watan Fubrairu, 2021 Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban ‘yan majalisa. Bayan wani ‘dan lokaci majalisar dattawan ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arziki zagon-kasa. Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisar.