Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya bayyana yadda ‘yan sanda suka cafke dagacin garin Tungan Iliya dumu-dumu tare da mahara a wajen bata-kashi da ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun tirke gungun mahara a maboyan su cikin dajin Tunga Iliya, a nan ne fa bayan sun bude musu wuta, suma maharan suna maido wuta, har Allah ya baiwa ‘yan sanda sa’ar fin karfin su.
Bayan ‘yan sanda sun yi wa maharan zobe sai suka kutsa cikin dajin canciki inda suke boye, sai ko kwatsam suka iske harda Dagacin garin cikin maharan da shi ake ta batakashi da ‘Yan sandan.
An daɗe ana zargin wasu Sarakunan gargajiya da hannu a ayyukan ta’addanci a yankin Arewacin Najeriya, dalilin da ya sa ake ganin abubuwan da suka taimaka kenan wajen shawo kan matsalar.