Ƙungiyar Dattawan Arewa ta fito fili ta nuna rashin jin dadin ta akan sakon Kirsimeti da Shahararren Limamin addinin Kirista Bishop Kukah ya yi, inda ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Buhari.
Babban Bishop ɗin dake zama a Sokoto yanzu ya zargi Shugaban kasa da son kai, da nuna wariya ta ƙabilancin addini, inda ya tabbatar da cewar da wata kabilar ce tayi haka, da Najeriya ta kasance cikin yaki a yanzu.
A martanin da kungiyar ta Dattawan Arewa NEF ta fitar ta ce duk wanda baya farin ciki da Gwamnatin Buhari to ya tafi kotu neman haƙƙin shi ba surutai marasa amfani ba.
Ƙungiyar Dattawan Arewa ta nuna rashin jin dadin ta a kan maganganun Bishop Kukan na cewa da yayi a tsige Shugaban kasar da tsari wanda ba na mulkin dimokradiyya, bisa ga gazawarshi ta fuskar samar da tsaro a ƙasa.
Bishop Kukah ya koka a ƙaruwar hare-hare da kashe kashe da ake yi a kasar, ya ce idan da Musulmin da ba dan arewa bane Shugaban kasa sannan ya aikata abunda Buhari ya aikata, to da an yi juyin mulki da dadewa.
Kungiyar Dattawan Arewan a martaninta tace koda dai ta yarda da maganar Kukah na cewa gwamnatin Buhari bata mutunta wasu abubuwa, ba daidai bane neman mafita ga matsaloli ta tsarin da ya saba damokradiyya.
A cewar Dr. Hakeem Baba-Ahmed, daraktan kungiyar, Najeriya na fuskantar kalubale a karkashin Buhari ta bangaren zartar da hukunci. Sai dai, ya ce kungiyar bata goyon bayan kowane irin gwamnati baya ga wanda aka samu bisa takarkin damokradiyya.
A cewarsa, mafi akasarin mutane, hatta ga wadanda ke goyon bayan shugaban kasar, na burin ina ma ace yana ba da muhimmanci sosai wajen zabar wadanda yake ba mukami. Sai dai kuma, Baba-Ahmed ya kara da cewa duk wani dan kasa da baya farin ciki da gwamnatin Buhari to ya nemi gyara a kotu.