Kwararran masanin nan kuma mai sharihi kan al’amuran tsaro Group captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya, ya ce matsalar tsaron da ake fuskanta a Najeriya ta fi karfin jami’an tsaron kasar.
Group captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya, ya bayyana hakan a wata tattauanawa da ya yi da BBC, yana mai cewa “idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai”.
Yana cewa duka ko ta ina Najeriya ba ta da cikakken shirin da za ta fuskanci wadannan matsalolin a yanzu.
“Ko an ci gabala kan wadannan mutanen ta wani dan lokaci ce saboda suna dawowa bayan lokacin kadan,” in ji Group captain Sadiq.
“Babu isassun kayan aiki da sojojin Najeriya za su yi amfani da su don isa inda waɗannan mutanen suke, haka kuma da zukan da suke maƙalewa ciki sojojin ba za su iya shiga ba”
Da aka tambaye shi game da furucin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na bai wa hafsoshin sojin kayan aiki sai Group Captain Sadiq ya ce ” na ji dadin furucin shugaban amma wannan ba abu ba ne na kusa ganin cewa kayan ba a nan ake samar da su ba”.
Anan Group Captain Sadiq ya ce “Idan shugaba na magana a irin wannan lokaci da mutum biyu yake magana, na farko wadanda ya bai wa aiki cewa su kara kaimi, sai kuma wadanda hare-haren ke rutsa wa da su cewa su kara hakuri gwamnati na iya ƙoƙarinta wajen wannan yaƙi”.
“Akwai tarnaki wajen cewa gwamnatin Najeriya take da shi na maganar tsaro, ba zai zama laifi ba idan ana ce mata babu abin da ta yi sai ta kara himma a nan gaba”.
Wannan na zuwa ne dai dai lokacin da Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da 8,000, kana an raba wasu fiye da 200,000 da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekaru kimanin goma.