Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma’a a jihar ‘Allah ya isa’.
Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga ‘yan jiharsa a yammacin Talata.
A cewarsa, “Ko a makka ba za a yi sallar idi ba amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni amma ba zan yafe wa wanda yayi min kazafi ba.
” Gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai bar kowanne mutum shiga jihar Kaduna a ranar Sallah daga Kano ba. Kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma’a.
Da kaina zan je hanyar shigowa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana da Cutatar da tayi katutu a tsakanin mutane. Mu kuwa ba za mu bari su shigo mana da ita ba. Ba zai yuwu ba,” in ji El-Rufa
Har ila yau, gwamnan ya zargi jami’an tsaro da cin amana inda ya ce suna karbar na goro domin barin jama’a su shiga jihar Kaduna.
Gwamna Nasir ya ki sanar da lokacin da ake tsammanin bude jihar.
Mataimakiyarsa ta ce har yanzu basu gamsu da yanayin da cutar take ba ballantana su bude jihar.
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin dadinta da yadda ake samun sabani tsakanin wasu jihohi da kuma matakan da take dauka a kan yaki da korona a kasar nan.
korafin na zuwa ne bayan tsawaita dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin tarayya ta yi wa jihar Kano na makonni biyu.
A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da wasu gwamnonin jihohi ta yanar gizo a kan yaki da cutar korona tare da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaron kasar nan.
Shugaba Buhari ya nemi hadin kan jihohin inda yace gwamnatin tarayya na tufka amma wasu jihohin na warwarewa.
[covid-data]