- Domin Kawo Karshen Boko Haram Zamu Dauko Sojojin Kasar Chadi Da Kamaru Amatsayin Haya.
Yaƙi Da Boko Haram Ya Kusan Zuwa Ƙarshe, Zamu Kawo Sojojin Ƙasar Chadi Dan Su Taya Mu Aiki, Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Janar Attahiru
Shugaban sojojin Najeriya, Maj Gen I. Attahiru ya bayyana cewa kwanannan za’a kawo ƙarshen yaƙi da Boko Haram.
Ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kaiwa sojoji a jihar Borno inda yace yana sane da matsaloli da suke fuskanta na ƙarancin kayan aiki da daɗewa a fagen daga amma yana musu alƙawarin duk za’a shawo kan matsalar nan ba da jimawa ba.
Ya kuma yi musu alkawarin cewa, zasu kawo sojoji ƙasar Chadi dan a hada kai a kawar da matsalar tsaron baki dayanta.
“Kwanan nan nake sa ran za’a gama yaƙin dan kowa ya koma zama da iyalansa.” Inji shi