NDLEA ta Kama Hodar Iblis Mai Nauyin Kilogiram 43.11 wadda aka kiyasta Kudin ta da Bilyan Talatin da Biyu…..
Hukumar Hana Sha da fataucin Miyagun kwayoyi ta NDLEA tayi Nasarar chafke wasu masu ansar kaya a Gabar Ruwan Legas ta Tincan Island.
Shugaban da yake Kula da Gabar Ruwan Sumaila Ethan shine ya bayyana ma Manema Labarai cewa kayan sun kwana biyu da zuwa daga kasar Brazil amma masu su basuzo ba domin tantance wa su dauka, Jami’an Hukumar sunata zuba Idanu Dan ganin wanda zaizo domin karbar kayan Inda su wadannan masu kar’bar ko clearing agent suka zo domin su fitar da kayan.
Yace bayan da aka kamasu an samu Daurin Hodar Iblis Kimanin guda Arba’in a cikin Jirgin ruwan mai Lamba MV SPAR SVORPIO wadda aka boye a tsanaki.
Bayan kammala Bincike a Dakin gwaje gwaje an gano cewa Hodar Iblis ce, an kuma kullesu ana cigaba da Bincike.
Wannan Nasarar dai tana zuwa ne tun bayan da aka kama irin wadannan kayan a Filayen Jiragen Saman Abuja da na Legas, kazalika da kamun kayan maye kala kala a Jihohin Edo Katsina Nasarawa FCT dama Benue