Bikin cikar Iran shekara 42 da samun nasarar juyin juya halin musulunci.
An yi holen makamin nan da aka yi amfani da shi wajen kakkabo jirgin Amurka mafi tsada da fasahar zamani mai suna “Global Howk”
Sannan kuma aka yi karin haske ga duniya game da yadda rundunar IRGC dake kula da tsarin tsaron sararin samaniyar Iran suka harbo jirgin a watan Juni na 2019
–
Makamin mai suna ‘Khordad-3rd” an dade da kera shi,kana aka ajiye shi domin irin wadannan ofireshin din,kuma sai da injiniyoyin sojan IRGC suka gama gano fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera waccan jirgin dan lele,kafin kuma a kera masa irin nasa makamin saboda an san watan wataran zai iya kawo latsi ga Iran.
–
Rundunar IRGC din tayi Karin bayani game da yadda aka tsara ofireshin din cikin basira da nutsuwa kafin daga bisani a kakkabo jirgin. Shi dai wannan jirgi mai suna RQ-4C Global Hawk’ an kera shi ne domin aikin soja da leken asirin sirri mai zurfi,kuma an kashe kudi kimanin Dalar Amurka miliyan $200 wajen kera shi. Yana iya sajewa da yanayin sararin samaniya mai yawa ba tare da an gano shi ko an jiyo tafiyarsa ba.
–
Suka ce a wata ranar Laraba ne wannan jirgin ya taso daga wani sansanin sojan Amurka boyayye a kudancin tekun Farisa da misalin 19:44 agogon GMT
Kana sai ya kashe dukkanin na’urorin dake jikinsa domin kar ma a iya kamo radiyonsa ko a jiyi tafiyarsa ko a iya shinshinar safarinsa.
–
Sai ya biyo ta gabar ruwan CHABAHAR ta yankin mashigin ruwan HORMUZ cikin labe da sassarfa. Yayin da yake kokarin komawa gabashin yankin ruwan,bayan ya gama nadar wasu bayanan sirri tare da daukar wasu hotuna ta hanyar wasu boyayyun kamarorinsa. Sai ya shiga yankin kasar Iran, nan ma sai ya rika karbar sakonni tare da daukar wasu bayanan sirri,amma ba tare da ya san cewar tun tasowarsa Rundunar IRGC na bibiyar takunsa ba.
–
Nan take su kuma rundunar IRGC dake kare sararin samaniyar Iran din suka harbo shi da misalin karfe 23:35 agogon GMT da wannan makamin mai jiran ko-ta-kwan na IRGC,sannan suka kwashe ragowar kwanson jirgin zuwa dakin bincike na ‘IRGC Aerospace Forces unit’
Wannan lamarin ya tozarta Amurka ta fuskar tsaro da aikin soja matuka gaya,ya kunyata ta a idon duniya matuka. Kuma harbo jirgin ne ya kawo karshen duk wata fatar da Amurka ke da ita ta yakar Iran din da karfin soja.
–
Shi wannan makamin yana iya raba kansa zuwa gida 4 a lokaci daya domin bibiyar hadafinsa. Yakan yi hakqn ne koda abokan gaba zasu nemi su raba masa hankali yayin da ya tunkaresu.
Tunda wasu jiragen suna iya yin dakon wasu kananan jiragen a mukamukinsu ta yadda Idan sun shiga hatsari sai su yan kananan su fice da wasu bayanan sirrin da babban nasu ya nada,koda kuwa shi babban zai rasa ransa.
–
Bayan harbo Wannan jirgi dan lelen Amurka,kwamnadar rundunar IRGC, Manjo Janar Husaini Salami ya bayyana cewar,harbo jirgin na dauke da wani sako na musamman zuwa ga jagororin Amurka na cewar,duk takunsu bai wuce a cikin tafin hannun Iran ba. Duk da dai Iran bata nufin yin yaki,amma ta aike da sako mai gauni zuwa ga makiya domin su san cewar duk wani yunkurin su na kawo wa Iran hari ko latsi,to zai ci karo da martani mai gauni inji Janaral Salami.