Shugaban Bankin bayar da lamunin gidajen na kasa, Architect Ahmad Musa Dangiwa ya Sabunta rijistar sa ta shedar zama cikakken dan jam’iyar APC.
Arch. Dangiwa ya Sabunta katin nasa a rumfar zabe da ke makarantar firamaren dajin Dun du, a mazabar Galadima ‘B’ ta karamar hukumar Kankia jihar Katsina.
Ayayin gudanar da sabuntawa katin nasa Dangiwa ya samu tarba ta musamman daga al’ummar da suka halarci taron wadanda sukazo daga wurare daban daban cikin fadin jahar nan
Shugaban jam’iyar APC na shiyyar Funtua Alhaji Bala Abubakar (Chigarin Musawa) ne ya jagoranci sabunta rijistar ta Arct. Dangiwa da ya gudana ajiya tare da shugaban jam’iyar APC na shiyyar Daura Alhaji Usman Ossy.
Dayake zantawa da manema labaru bayan ya sabunta rijistar tasa Artc. Dangiwa Shugaban bankin Bayarda lamuni na kasa, ya bayyana jindadinsa akan yadda mutane suka fito kwansu da kwarkwata domin sabunta rijistar tasu.
Yakuma kum kara da godema gwamnan jahar katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta kan kokarinsa akan harkar matsalar tsaro da ta addabi jahar Katsina.
Bugu da kari Dangiwa yayi jinjina da yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan aikin layin dogo na tashar jirgin kasa da aka kaddamar aranar talata a cikin jahar Katsina.
Akarshen jawabin nasa Arch. yayi kira ga Al’umma dasu cigaba da bayarda goyon baya ga tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati domin cigaban jahar nan.
Anashi jawabin Shugaban jam’iyar APC na shiyyar Funtu kuma Chigarin Musawa Alh. Bala Abubakar yayi jinjina ga Shugaban bankunan bayarda lamunin Ahmad Dangiwa ta fuskar kawo hadin da yakeyi.In
Inda ya tabbatar da hadin kansu tare da samun cigaba a cikin jam’iyar.
Daga Karshe Chigarin Musawa yma kara kira ga Al’ummar Karamar hukumar Kankia da sufito su sabunta katin su na jam’iyar APC don cigaba da samun nasarar jam’iyar, a zabuka masu zuwa.