Kanwan Katsina Hakimin Ketare ya amince da irin gudummawar da ‘yan jarida ke bayarwa ga ci gaban jihar.
Alhaji Usman Bello Kankara na magana ne lokacin da ya karbi bakuncin jami’an kungiyar ’yan jarida ta kasa reshen Rediyo jihar Katsina a kan ziyarar godiya bisa nadin da aka yi wa daya daga cikin mambobinta Jamilu Hashimu Gora a matsayin Sarkin Labaran Kanwan Katsina.
Kanwan na Katsina ya nuna godiya ga ziyarar
Haka zalika Shugaban kugiyar reshen gidan rediyon daya daga cikin yayan kungiyar Khalid alhafiz Bakori ya godewa kanwan na Katsina kuma zasu cigaba da tuntubar shi akan kawo cigaba afannin aikin jarida.
Kanwa yakara dacewa nadin Jamilu Hashimu Gora ya kasance bisa cancanta.
Ya ce wanda aka nada ya yi aiki a matsayin wakilin shiyya a yankin kuma ya ba da gudummawa ga ci gaban yankin ta hanyar watsa labarai yadda ya kamata.
Alhaji Usman Bello Kankara ya bada tabbacin ci gaba da tallafawa aikin jarida domin cimma burin da ake bukata.
Tun da farko shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen gidan Rediyon jihar Katsina Khalid Alhafiz Bakori ya ce sun gamsu da nadin da aka yi wa daya daga cikin membobinta a matsayin Sarkin Labaran Kanwan Katsina don nasiha ta uba kan yadda za a ciyar da kungiyar.
Shugaban ya mikawa basaraken lambar girmamawa.