Sulhu tabbataccan abu ne a cikin Alkur’ani mai girma da Sunnah da ijmain malamai
Yin sulhu yazo kashi biyar a cikin Littafin Allah
- Sulhu tsakanin ma’aurata, Allah ta’ala yace :
وَإِنۡ خِفۡتُمۡ شِقَاقَ بَيۡنِهِمَا فَٱبۡعَثُواْ حَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهِۦ وَحَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصۡلَٰحٗا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيۡنَهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرٗا
Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma’auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa. - Sulhu tsakanin musulmi da suka sami saɓani da ɓarkewar rikici, na addini ko siyasa ko ƙabilanci, a ɗaiɗaiku ko jama’a ko ƙasashe. Allah ta’ala yace :
وَإِن طَآئِفَتَانِ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱقۡتَتَلُواْ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَاۖ فَإِنۢ بَغَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا عَلَى ٱلۡأُخۡرَىٰ فَقَٰتِلُواْ ٱلَّتِي تَبۡغِي حَتَّىٰ تَفِيٓءَ إِلَىٰٓ أَمۡرِ ٱللَّهِۚ فَإِن فَآءَتۡ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَا بِٱلۡعَدۡلِ وَأَقۡسِطُوٓاْۖ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ المقسطين
Kuma idan jama’a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.
-Surah Al-Hujurat, Ayah 9
-3. Sulhu tsakanin musulmi da kafurai, waɗanda suke yaƙar mu, sai a ƙulla yarjejeniya, zaman lafiya da fahimtar juna bisa wasu ƙa’idojin zamantakewa. Allah ta’ala yace:
وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.
-Surah Al-Anfal, Ayah 61. - Sulhu tsakanin tsakanin makota, da ƴan’uwa, da dangi. Allah ta’ala yace :
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã’a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai.
- Sulhu tsakanin masu hulɗa da juna ta kuɗi ko kasuwanci ko bashi, ko ajiya ko aro, ko rance, da sauran hulɗoɗi da suke faruwa tsakanin jama’a. : Allah ta’ala
لَّا خَيۡرَ فِي كَثِيرٖ مِّن نَّجۡوَىٰهُمۡ إِلَّا مَنۡ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوۡ مَعۡرُوفٍ أَوۡ إِصۡلَٰحِۭ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
-Surah An-Nisa’, Ayah 114
SULHU A CIKIN SUNNAH,
1,Manzon Allah saw ya kasance yana sulhunta masu rigima, ko rashin fahimtar juna.
2, Manzan Allah saw yace : Sulhu ya halatta tsakanin musulmi, face sulhun da zai halatta haram ko ya haramta halal, Abu Dauda( 3594) Tirmiziy (1352.)
SULHU TSAKANIN MALAMAI.
Dukkan malamai sun haɗu akan yin sulhu tsakanin al’umma ya dace da shari’a. da hankali da al’adu masu kyau na zamantakewa.
HANAFAWA, sunce: ana ƙulla sulhu domin kawar da gardama tsakanin al’umma.
نتائج الأفكار تكملة فتح القدير 8/403
MALIKIYYAH sunce: sulhu shine warware rikici ko kiyaye faruwar sa bisa wani hakki da ake nema. الشرح الكبير 530.
SHAFIAWA : sunce sulhu shine ƙulla yarjejeniya domin kawar da husuma.
حاشية عميرة 2/382
HANBALIYYAH sunce : sulhu shine : Shawo kan wata matsala da sulhuntawa tsakanin masu saɓani.
المغني 4/527
MANUFOFIN YIN SULHU
- Yin sulhu yana tsare addini, ya kawo zaman lafiya. Manzon Allah saw yace, shin bana baku labari ba gamai da wani abu wanda yafi darajar azumi da Sadaƙa da sallah sai sahabbansa suke ce muna so muji, sai yace sulhunta tsakanin ku, domin lalacewar zamantakewa itace mai aski, (wacce take kawar da zaman lafiya kamar yadda mai aski yake aske suma) Abu Dauda( 4919).
- Yin sulhu yana kawar da gaba da kiyayya wacce take kawo rashin zaman lafiya da yawan gardama da husuma tsakanin al’umma. Manzon Allah saw yace : Duk ranar Litinin da Alhamis ana buɗe kofofin aljanna ana yin gafara ga dukkan musulmi wanda baya shirka face masu gaba da juna za a ce a kyale su har sai sun shirya, Muslim 2565.
KUYI BIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER