Sakamakon rahotanni da aka samu dangane da kalamai na tunzura Jama’a da ka iya kawo tashin hankali da sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ke yi majalisar zartarwar Kano ta umarci da a gaggauta rufe masallaci da cibiyar da yake gudanar da karatukansa a filin mushe da duk wani waje da ya ke yi a fadin jihar har Sai jami’an tsaro sun kammala binciken da suke gudanarwa a kai.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan a Daren yau Laraba a fadar gwamnatin Kano yayin da yake zantawa da manema labarai.
Malam Muhammad Garba ya kara da cewa majalisar ta kuma umarci shi da dakatar da wadannan wa’azi da yakeyi na rashin Kan gado.
Majalisar ta kuma umarci kafafen yada labarai dana sada zumunta da su dakatar da sanya karatukan sa don tabbatar da samun zaman lafiya a jihar Kano.
KUYI BIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER