Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
A cigaba da matsalar tsaron da ke addabar wasu yankuna na jihar Katsina wanda yanzu abin ya dauki wani sabon salo ta yadda kullin sai ka ji labarin an kashe mutun ko an sace ko an kori dabbobin mutane ba tare da daukar mataki ba.
Wannan lamari ya qazanta fiye da sauran lokota a baya, abinda kowa ya sani shi ne, gwamnatin tarayya da kuma ta jiha suke da alhakin bada kariya ko tsaro akan al’ummar da suke shugabanta, saboda haka duk abinda ya samu shamowa watan bakwai ya ja ba ta.
A bisa wannan qiyasa kowa na da tunanin babu wani abu da ya fi karfin gwamnati musamman wannan gwamnatin da ta zo tana cewa tana sane da duk wata matsala da ta shafi harkar tsaro musamman a arewacin Najeriya, Katsina kuma ita ce uwa a wannan lokaci.
Saboda haka uzurin da za a iya yiwa wannan gwamnati an riga an yi, abinda kawai ake so a gani shi ne, aiki a aikace, idan kuma ba a gani ba, to lamarin ya qazanta domin ana buqatar bayani wanda zai gamsar da jama’a akan halin da ake ciki.
Kamar yadda na ambata haqqin samar da tsaro ya rataya ne akan gwamnatin tarayya da kuma ta jiha wani lokaci da har da su kan su al’umma domin su ne abin zai yi wa daxi idan akan samu nasara, idan kuma aka samu aqasin haka sune ne waxanda za su xanxana kuxar su, Allah ya sawaqe.
Tarihi ya nuna yadda wannan gwamnatin ta jihar Katsina ta gaji matsalar tsaro daga gwamnatin da ta gabata, sai dai bata tsaya yin wata-wata ba, lokacin da suka shiga ofis sun fara kallon yadda za su bulluwa wannan lamari domin idan har ba a samun zaman lafiya ba, to tafiyar da gwamnatin zai zama wani baban qalubale a gareta.
Bayan yin dogon nazari game da wannan batun wanda yake da matuqar mahimmacin a rayuwar duniya, an fara kallon abin ta fuskar lalama sannan daga bayan maganar sasanci ta shigo wanda kowa yana san irin rawar da gwamnatin jihar Katsina qarqashin jagorancin Aminu Bello Masari ta yi na ganin an kawo qarshen matsalar tsaro a jihar Katsina .
Wannan duk ya faru ne, tare da cewa gwamnatin tarayya ita ke da alhakin yin hakan, amma kafin gwamnatin tarayya ta waiwayi jihar Katsina akan maganar matsalar tsaro tuni lamarin ya fara zama wata annoba ta musamman.
Ko kafin xaukar wancan matakin na sasanci da kuma sulhu sai da aka sanar da gwamnatin tarayya ta amince sannan aka yi haka, amma dai har yanzu kamar jiya kamar yau, inda ake dai nan ake, har qara ma ace gwamma jiya da yau.
Mun sha jin cewa shugaban qasa Muhammadu Buhari yana bada umarnin a turo jami’an tsaro jihar Katsina domin ganin an kawo qarshen wannan matsala, shima da kansa sau uku yana bada umarin ga sojojin da ke aikin kawo zaman lafiya a jihar Katsina umarnin ko wa’adin sati uku su kawo qarshen wannan matsala amma shiru kake ji kamar an aiki Bawa garinsu.
Haka kuma vangare su kansu al’ummar da wannan bala’I ya shafa sun fara fidda rai da daga gwamnatin tarayya zata fidda su daga wannan matsala da ta yi alqawari tun kafin a zave ta, amma har yanzu babu labari, sai na bakin ciki.
Kazalika mun sha jin cewa gwamna Aminu Bello Masari yana faxan cewa gwamnatinsa na kashe aqalla naira miliyan sitin duk wata akan matsalar tsaro kuma ba mu tava jin su jami’an tsaron sun musanta hakan ba, to amma me yasa wannan lamari kullin sai qara gaba yake?.
Sannan muna ganin irin yadda gwamnatin jihar Katsina ke faman xawainiya da jami’an tsaron da ake turuwa daga Abuja domin yin wannan aikin amma fa maganar kullin xaya ce babu tsaro, kullin sai an kai hari, sai an kashe, sai an sace shanu da mutane domin neman kuxin fansa.
Mutanen Katsina sun yi kuka har sun gaji akan wannan matsala amma hukumomin tsaron da wannan matslaar ta rataya akan su, sun yi gum da bakin su, sun ki yin abinda ya kamata su yi akan wannan batu mai matuqar mahimmaci ga wannan al’umma.
Idan muka duba yawan sojojin da aka kawo Katsina ko waxanda ake da su gaskiyar magana ba za su iya tunkarar waxancan mutanen masu manyan makamai masu linzami na qare dangi da suke xaukar fiye da awa biyar suna kai hare-hare ba tare da wani jami’in tsaro ya tunkari inda suke ba.
Anan muna shaidawa duniya cewa abubuwa da suke faruwa jihar Katsina akwai sakaci da rashin kula da yin watsi ko shakulatan vangaro da sha’anin tsaro a jihar da shugaban qasa ya fito kullin ana kashe su ba ji ba gani, kuma ko damuwa ba sa nunawa wannan abu akwai takaici so sai.
Koda jihar Katsina ba jihar Buhari ba ce, suna da haqqin a samar masu da tsaro a matsayinnsu na wani vangare na Najeriya, saboda haka a qa’ida ba sai sun liqa kansu da shugaban qasa ba, jami’an tsaron Sojoji sun ki yin abinda ya kamata wani lokacin a gaban idon su ake kashe mutane, amma da zaran an kai masu rahoto sai ka ji sun ce ba a ba su iznin xagawa daga inda suke ba.
Wani abin ban takaici da bakin ciki shi ne, irin yadda a wasu lokuta ake amfani da kuxaxan qananan hukumomin da wannan matsala ta shafa wajan samar da kuxin alawus alawus da waxannan Sojoji da aka jibge da sunan aikin samar da tsaro.
Gwamnatin jihar Katsina da kanta ta fito fili ta koka akan yadda duk abinda jami’an tsaro ke buqata wanda za su yi aikin samar da zaman lafiya, amma abinda ake gani ba abu ne da za a amince da shi ya cigaba da faruwa ba, ganin yadda wannan abu ke qara qazanta. Idan muka koma akan maganar su kan su jami’an ‘yan Sanda magana ta gaskiya babu su isaso a wannan jiha ta ke fama da matsalar tsaro, wanda haka bai kamata ace ‘yan sanda ba su da kayan aikin tunkarar waxannan ‘yan ta’ada daga vangaransu.
A irin wannan hali ne, kullin sai dai ka ji mai taimaka wa shugaban qasa na musamman Malam Garba Shehu yana Allah wadai da irin abubuwa da ke faruwa a jihar Katsina da sunan shugaban qasa, wannan lamari da bakin cikin da ban takaici yake.
Saboda ganin irin wannan yanayi da ake ciki tasa hatta ‘yan majalisar jihar Katsina musamnnan waxanda suka fito daga qananan hukumomin da wannan matsala ta shafa sun fara hayaqa da shugaban qasa inda suke kiransa da nuna shi a matsayin mutumi da gaza a vangaran tsaro.
Sannan sun nuna a fili cewa wannan abu ba abinda za su yarda da shi ba ne, sun shirya tare da mutanen su za su yi fitofito da duk wanda yake da haqqin yin wani abu akan harkar tsaro amma yaki yi Har gobe mamaki da tambayar da jama’a ke yi wa kansu ita ce, me jihar Katsina ta yi Buhari, me gwamnatin Katsina ta yi shugaban qasa, me yasa ya kauda kai daga taimakon su akan matsalar tsaro, me yasa ya zuba ido ana ta kashe al’umma kullin rana ba wani mataki daga vangaransa?
Yanzu dai duniya na kallo, kungiyoyi kare haqqin xan adam suna ji, kuma suna kallo, shima shugaban qasa yana ji ko kuma yana kallo, sannan al’umma suna ji suna kallo.
A qarshe qarshe Allah Yana ji kuma yana gani sannan shi ka xai ya san dalilin da yasa Buhari baya nuna damuwa da abubuwan da ke faruwa na matsalar tsaro a jihar Katsina
[covid-data]