Lauyoyin sun rubutawa shugaban gidan wannan jarida watau Omoyele Sowore takardar ne a dalilin wani labari da ya buga kwanaki na cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya rasu.
Lauyoyin sun bayyana cewa labarin karyar da jaridar ta buga a ranar Lahadi na cewa Sheilh Bala Lau ya mutu a sanadiyyar kamuwa da ciwon COVID-19 ya cutar da babban malamin.
A wannan labari na bogi, jaridar ta bayyana cewa an sabawa umarnin da gwamnati ta bada na gujewa cinkoso da samun tazara wajen birne malamin, wanda hakan bai tabbata ba.
Lauyoyin sun ce shugaban na kungiyar JIBWIS na kasa ya koka da cewa wannan rahoto da aka fitar ba komai ba ne face karya, zalunci, yaudara, sharri da kokarin ci masa mutunci
A wannan takarda, lauyoyin sun tabbatar da cewa malamin ya na nan a raye cikin koshin lafiya a garin Jimeta da ke jihar Adamawa, inda ya ke gabatar da tafsiri ga tarin mabiyansa.
Yayin da ake fama da annobar COVID-19 a Duniya, lauyoyin sun bayyana cewa ko kwarzane bai kama shehin malamin ba, har ta kai a fara yada jita-jitar cewa ya mutu da rana tsaka. Takardar ra ce: “Wajen gaggawar da ku ka saba na buga labari, kun yi ganganci, ba ku tabbatar da bayanan da ku ka samu ba, dalilin haka ku ka jefa wanda mu ke karewa a takaici.” Kamar yadda mu ka samu labari, lauyoyin sun zargi gidan jaridar da jefa dinbin mabiyan kungiyar da Lau ya ke jagoranta cikin wani irin yanayi a sakamakon wannan labari.
Don haka aka bukaci jaridar ta fito ta janye wannan labari, ta bada hakuri a gidan jaridu shida da harshen Ingilishi da Hausa.
Sannan ta biya tarar Naira miliyan 100 cikin mako guda. Bayan haka an bukaci gidan jaridar su bada hakuri a gidajen rediyon arewacin Najeriya da kasashen Nijar, Ivory Coast, Ghana da sauran kasashen Afrika da Izala ta ke da mabiya.