Kwaminshinan Ma’aikatar Tsumi Da Tanadi Na Jihar Katsuna Hon. Faruk Lawal Jobe Ya Sabunta Katin Zama Dan Jam’iyyar APC.
Kwaminshinan afannin tsumi da tanadi na jihar Katsinan Hon. Faruk Lawal Jobe ya sake sabunta katin zamanshi dan jam’iyyar nashi ne a rumfar zaben dake kofar fada (Read Room)atsakiyar garin Kankara ayau.
Ayayin sabuntawar Hon. Kwaminshinan yayi samu tarba ga al’ummar wannan yankin da rumfar zaben take hannu bibiyu.
Haka zalika Hon.Jobe ya samu rakiyar wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar ta APC wadanda suka hada da Hon. Ibrahim Ahmed Danmasanin Kankara,Jamilu M.Kankara dadai sauran masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar ta APC na wannan yakin.
Bayan kammala aikin sabuntawar Mai girma kwaminshinan tsumin da tanadi ya nuna godiyarshi matuka abisa yanda al’unma maza,mata,matasa da tsofaffi na tururuwar zuwa rumfar da ake gudanar da wannnan nuhimmin aiki.
Bugu da kari Mai girma Jobe yayi kira da babbar murya ga al’umma da su cigaba da sabuntawa gamida yin sabuwa ga wadanda basuda ita tun fil’azal.
Ata bakin daya daga cikin jigogin jam’iyyar ayankin karamar hukamar mulkin Kankara Hon. Ibrahim Ahmed Dan-masanin Kankara ya bayyana farin cikin shi ata fuskar yanda suka ga al’umma nata kokarin ganin sun samu damar mallakar rijistar zama ‘ya’yan jam’iyyar APC, Dan-masanin na Kankara yayi wannan jawabine ayayin zantawar shi da wakilinmu ayau.
Yakuma kara da cewa ayanda aikin ke tafiya yazama wajabi akaro tikitin yin rijistar.
Daga karshe mai girma Faruk Lawal Jobe ysyi fatan alheri da samun dauwamammen zaman lafiya mai dorewa.