Rana ta biyu a Garin Dikwa Zulum ya Raba kuɗi, da Abinci a Dikwa.
Rana ta biyu a Garin Dikwa Zulum ya Raba kuɗi, da Abinci a Dikwa. Maigirma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana...
Fitacciyar tsohuwar jarumar Hausa Fim ta Kannywood, Saima Muhammad, ta ce ko gobe ta samu mijin aure, za ta shiga daga ciki ba tare da ɓata lokaci ba.
Jarumar ta dade tana jan zarenta a masana’antar, duk da cewa ba kowane irin fim take fitowa ba, kasancewar ta ce sai ta zabi fim din da zai koyar da mutane abin kirki.
Ga wadanda suka san jarumar, sun san irin rawar da ta taka a masana’antar. Hakazalika an daina jin duriyarta daga baya.
Jarumar ta ce, ta dau hutu ne don ganin an samu sauye-sauye a yanayin fina-finan masana’antar, wanda ya saɓa da yadda aka san shi a baya.
A cikin fina-finan da jarumar ta taka rawar gani kuma ya yi fice akwai fim din Zuri’a. Jarumar ta fito a matsayin matar Ali Nuhu, daga baya ta kamu da cutar sankarar nono wadda saboda hakan ta umarci maigidanta da ya auro Zainab Indomie.
Da kyar ta rika rokon Zainab Indomie din da ta auri mijinta saboda muguwar cutar da take dauke da ita. Daga bisani sai ta amince don aurenshi.
A wata hira da Saima ta yi da BBC, ta bayyana cewa ta shiga Masana’antar Kannywood ce domin son ci gaba da kuma kokarin yin wani abu mai kyau da mutane za su rika tunawa da ita.
Sannan ta ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, inda ta ce tana fata Allah Ya kawo mata miji.
“Na shiga masana’antar ce saboda ina son ci gaba, ina son yin wani hobbasa mai kyau da mutane za su gani su yi koyi da mu.
Ko lokacin da na fara, idan ka kawo min labarin fim, idan na ga shirme ya fi yawa sai in ce ba zan yi ba. Ko a baya-bayan nan, an rika magana a kan an cika waka da sauransu.
Sai na dauki hutu in je in dawo, watakila idan na ga abin ya yi min sai in ci gaba. “Har na je Kaduna na yi fim guda daya, amma kamar yadda na fada sai na zabi fim da nake so.
A zo a ce kawai an kawo wane ne mijina, za mu fito mu yi ta rawa muna waka. Ba zan karbi wannan ba. Zan karbi wanda zai koyar da mutane wani abu ne.
Daga nan sai na yi aure, na auri wani dan asalin kasar Kongo Brazabille, amma mun rabu.” Game da sake aure Saima ta ce, “Aure rai ne da shi. Allah ne Ya halicci aure, Ya halicci saki duk da cewa ba Ya son saki.
Dole sai an yi hakuri domin zama da mijin yanzu. Duniya ce ta zo karshe, ba wai ’yan Kannywood ba ne kawai. Amma da yake mun fito da kanmu duniya, shi ya sa ake ganinmu. Amma ba a kanmu ba ne kawai. “A taya ni da adu’a, a matse nake inyi aure.
Abubakar Ismail Kankara is an accomplished investigative journalist, fact-checker, seasoned storyteller, PR professional, skilled video editor, website designer, and proficient in SEO/Social Media Management. Additionally, he is a 2023 Govspend Media Fellow and a 2024 UDEME Accountability Fellow.
Rana ta biyu a Garin Dikwa Zulum ya Raba kuɗi, da Abinci a Dikwa. Maigirma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana...
Magu Ya Taya Sabon Shugaba Murna Sabon Shugaban Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa yace tsohon Shugaban...
Kuskure Ne Tantance Tsoffin Shugabannin Tsaro – Sani Tsohon Sanatan Jihar Kaduna Sanata Shehu Sani, ya soki lamirin majalisar Dattawa...
Dikko Shine Yayi Kokarin Gyara Ingantuwar Hanyoyin Shigar Kwastom Kanwan Katsina, Alh. Bello An bayyana...
Copyright © 2024 DAILY EPISODE Designed by AIACCESS CONTRACTORS
Copyright © 2024 DAILY EPISODE Designed by AIACCESS CONTRACTORS