Dan majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kankara,Faskari Da Sabua Ya Sabunta Rijistar Zama ‘Dan Jam’iyyar APC A Katsina.
Dan majilisar wakilai ta tarayya Hon. Murtala Isah Kankara wanda akewa lakani da (Mai nauyi)ya sabunta rijistar shi ta zama dan jam’iyyar APC mai mulki, wannan sake sabuntawar ta kasance ne ajiya) arumfar zaben babbar makaratar firamare Nuhu Model dake
cikin garin Kankara jihar Katsina.
Ayayin sabuntawar mai girma Danmajilasar mai wakiltar kananan hukomin ukku daga yankin Katsina ta Kudu (Funtua Zone) wadanda suka kunshi Kankara,Faskari da Sabua yasamu tarbar daru ruwan al’ummar masoya daga kauyuka na yankunanan dayake wakiltar a majilasar tarayya musanman na karamar hukumar Kankara.
Wasu suka rufamasa baya yayin sabuntawar sun hada daga cikin shuwagabannin jam’iyyar ta APC Reshen karamar hukumar ta Kankara irinsu shugaban riko na jam’iyyar a Kankara Alhaji Badamasi Pauwa, sakataren jam’iyya Hon.Mansir Ishaq Jery , babban jigon jam’iyyar Hon. Bello Bello Gimba Kungiyar matasan Jam’iyyar reshen karamar hukumar ta APC Vangurd wasannin sarkin pauwa Hon. Hamza Bagadaza da dai sauran masu ruwa da tsaki ajam’iyyance.
Bayan kammala sabutawar Hon. Murtala Isah Kankara ya nuna matukar farin cikin shi ayadda yaga aikin na sabuntawar na tafiya ka’in da na’in yakuma jinjina ma shuwagabannin jam’iyyar ta APC na rashen Karamar hukumar ta Kankara abisa jajircewarsu afannin wayewar ds al’umma kai na muhimman cin sabuntawar rijistar.
Hon. Mai nauyin ya ziyarci wasu wurare dake cikin garin na Kankara wadanda suka hada da Unguwanni Dan dutse domin ziyartar gsisuwar wani rashi da akayi na wata Mata ,Unguwar Mangwarori domin ta’aziyar rashi dadai sauran wuraren akayi rashe rashen rayuka inda ysyi addu’ar Allah ya gafartawa dukkanin musulmin da aka rasa rayukansu baki daya.
Daga karshe Dan majilasar tarayyar karshe yayi godiya da irin tarbar nuna kauna da yasamu ka jama’ar garin kankara,yakumayi kira da afito a yankin katin zama ‘ya’yan jama’iyyar APC.