Kasuwar Musayar ‘Yanwqsa: Makomar Son da Ramos da IbrahImovic.
Duk da cewar an rufe hada-hadar musayar ‘yanwasa musamman a nahiyar Turai amma kuma wasu kungiyoyin kwallon kafan sun sake daura damara domin sake yin cinikayya a karshen kakar wasa ta bana.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mourinho ya yi amanna cewa zasu sabunta kwantiragin Son Heung-min, dan wasan kungiyar mai shekara 28 wanda wa’adinsa zai kare a shekarar 2023 na bukatar hakuri da dabara a cewar jaridar Evening Standard.
Raunin da dan wasan baya na kasar Sifaniya Sergio Ramos ya ke fama da shi na iya janyo jinkirin sabunta kwantiraginsa a Real Madrid har zuwa lokacin da zai warke inda wa’adin dan wasan mai shekara 34 za ta kawo karshe a karshen wannan kakar wasan ta bana inji jaridar Marca.
Kocin Crystal Palace Roy Hodgson na sa ran kungiyarsa ta dauko Wilfried Zaha a karshen wannan kakar wasan, ganin cewa dan wasan mai shekara 28 kuma dan kasar Ivory Coast na sha’awar buga wasannin gasr Zakarun Turai a cewar jaridar Mail.
Manajan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Stefano Pioli ya ce ya dace a ce Zlatan Ibrahimovic dan wasan gaba mai shekara 39 ya ci gaba da buga wasanni tare da kungiyar ta Italiya. Wa’adin dan wasan mai shekara 39 zaizo karshe a karshen wannan kakar wasan inji jaridar Sky Sports.
Shugaban sashen kwallo na Ajax Marc Overmars ya kusa sauka daga mukaminsa a karshen wannan kakar wasan, inda a ke hasashen zai iya komawa tsohuwar kungiyarsa Barcelona ko Arsenal a cewar jardiar Mundo Deportivo.
Dan wasan tsakiya na Faransa Tanguy Ndombele mai shekara 24 ya yarda cewa dole ya sauya salon wasansa idan yana son samun nasarori a Tottenham, wannan labari jaridar Telegraph ce ta rawaitoshi.
Dan wasan Chelsea da Jamus Timo Werner mai shekara 24 bai iya zura kwallo ko daya ba a wasanni 14 da ya buga a gasar firimiyar Ingila. Amma ya ce ya yi imani lokaci na zuwa da zai koma ganiyarsa, inji jaridar Evening Standard.
Tsohon alkalin wasan gasar
firimiya Mark Halsey ya ce
amfani da fasahar VAR na kawo
sauye-sauye saboda zamani,
amma ya ce tilas a tausaya wa
alkalan wasan wadanda sun kusa
kasa wa saboda gajiya a cewar
Jaridar Sun.