Gwamnatin jihar Kaduna ta maida Almajirai ‘yan asalin jihar Zamfara 45 zuwa garin Gusau.
Kwamishinan harkokin yara, mata da ci gaban al’uma Zainab Lawal ta karbi wadannan almajirai a madadin gwamnati jihar Zamfara.
Duka wadannan almajirai an taho da su ne daga garin Zariya inda daga cikinsu akwai maza 28 da mata 17 kuma an karbe su a sansanin alhazai dake garin Gusau ranar Litini.
Ta kuma ce gwamnan Bello Matawalle ya kafa kwamiti domin kula da walwala da kuma ganin cewa duk almajiran da za a dawo da su an kai su ga iyayensu.
Zainab ta yi kira ga iyaye da su daina tura ‘ya’yansu wani gari ko kuma jihar yin barace-barace da sunan karatun addini.
Bayan haka kwamishinan yada labarai Sulaiman Tunau ya ce an yi wa duk almajiran gwajin cutar korona kuma dukkan su basu dauke da cutar.