A yau Laraba ne lokacin taron majalisar zartarwa ake sa ran Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai nada shugaban ma’aikatan fadarsa, tun bayan rasuwar Mallam Abba Kyari.
A ranar 17 ga watan Afrilu ne dai Allah ya yi wa Mallam Abba Kyari rasuwa sakamakon cutar korona.
Abba Kyari ya rasu ne a Legas, inda ya koma can bayan ya kamu da cutar korona domin ci gaba da jinya.
Da ma rahotanni sun ce Abba Kyari yana fama da wata rashin lafiya kafin ya kamu da cutar korona, kuma masana harkar lafiya sun ce masu fama da wata cutar na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga cutar ta korona.
Abba Kyari ya kasance mutum mai karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Buhari.
Dan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon dan jarida ne, kuma tsohon ma’aikacin banki, inda ya rike manya-manyan mukamai a wasu bankunan kasar.
Yanzu abun jira agani shi ne ko mutumin da zai gaji wannan gogaggen ma’aikacin yana da irin haibar da marigayin yake da ita.
‘Yan kasar dai na ta faman hasashe dangane da mutumin da zai maye gurbin marigayi Abba Kyari, inda a yau din nan za a tabbatar da hasashen nasu ko kuma akasin haka.