Hukumar asibitin ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta bai wa manema labarai a ranar Talata.
Kamar yadda takardar ta bayyana, majinyaciyar korona din ta haifa yaro namiji a ranar Asabar da ta gabata.
Amma kuma, ba ta bayyana cewa ko jaririn yana dauke da muguwar cutar ba. Takardar ta ce, “Kungiyar likitoci da ma’aikatan jinya sun karba haihuwar wata mata da ke dauke da cutar COVID-19.
Ta haifa yaro namiji mai nauyin 2.6Kg. “Matar mai shekaru 37 ta haihu ne bayan likitoci sun fede ta a ranar Asabar, 9 ga watan Mayu. Mahaifiyar da jaririn suna cikin koshin lafiya. “Muna taya dukkan ma’aikatan lafiya da ke sahun gaba murnar wannan nasarar
Wannan haihuwar an yi ta ne a yayin da ake tsaka da annobar korona a jihar Legas, jaridar The Punch ta ruwaito.
A ranar 11 ga watan Mayu, hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta ce jihar Legas na da mutum 1,933 da aka tabbatar suna dauke da cutar korona. 1,398 daga ciki har yanzu suna dauke da cutar, 502 sun warke sai 53 suka rasa rayukansu
A ranar 27 ga watan Afirilu, wata majinyaciya mai shekaru 40 ta haifa yarinya mace a asibitin.
Allah mai iko: Yadda mai jinyar korona ta haihu a asibitin Najeriya. Hoto daga The Punch Source: