Yau Talata Majalisar Dokokin Faransa za ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar dokar da za ta yi yaki da masu tsatsauran ra’ayin addinin Islama, wanda hukumomin kasar suka ce za ta tabbatar da matsayin kasar wadda ba ruwan ta da addini.
Shugaba Emmanuel Macron da ke hangen sake tsayawa takara ne ke jagorancin dokar wadda za ta mayar da hankali kan batutuwa da dama da suka hada da koyar da addini da yakar kyamar da ake nunawa masu auren mata sama da guda a intanet.
Ana saran ‘yan Majalisun su kada kuri’a yau da rana bayan kwashe sa’oi 135 ana tafka mahawara akan kudirin dokar.
Sabuwar dokar dai ta haddasa cece-kuce a tsakanin mabiya addinin Islama da ke kasar ta Faransa wadda ke ikirarin ba ruwanta da addini a lamurranta, ko da ya ke kungiyar musulmin kasar ta ce dokar ba ta yi karan tsaye ga tanade-tanaden addini ba.