Matar ta cinnawa gidan wuta ne a lokacin da ‘ya’yanta ke makaranta kuma mijinta na wurin aiki.
Matar wadda ‘yar Kenya ce kuma mai matsakaicin shekaru daga yankin Baraton da ke Kiminini, Trans Nzoia County ta cinnawa gidan aurenta wuta bayan tayi zargin mijinta zai ka aure.
Edina Ng’eno ta cinnawa gidan wuta ne da misalin karfe 9:30 na safe lokacin da mijinta, Elijah Nandwa Lomeni, ke wajen aiki da yaransu kuma na makaranta.
A cewar rahotanni, Edina ta kasance tana kwana a gidan kawarta bayan sabani da ta samu sabani da mijinta kan karo auren mata ta biyu.