Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbaci da lokacin da za a kawo karshen yaki da Boko Haram da ‘yan bindiga a Nijeriya, ‘yan ƙasa su cigaba da walwala cikin natsuwa ba tare da wata fargaba ba.
Shugaban kasar, wanda ya bayyana haka a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, ya ce za a kammala yaki da ta’addanci a karshen shekarar 2021, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.
Harkar tsaro dai ta ƙara shiga cikin wani hali tun bayan hawa mulki na shugaban kasa Buhari, inda kafin zuwan shi matsalar tsaro tana sashin Arewa maso gabashin kasar ne wato fitinar ‘yan Boko Haram.
Sai dai daga baya ayyukan ta’addancin sun faɗaɗa zuwa sashin Arewa maso yammacin kasar, wato Jihohin Zamfara Katsina da Jihohin Kaduna da Sokoto, sannan matsalar ta tsallaka sashin wasu Jihohin da ke sashin tsakiyar Najeriya kamar Jihohin Neja da Filato da Jihohin Binuwai da Taraba.
A shekarar da ta gabata ne aka ruwaito daga bakin shugaban dakarun sojin ƙasar janar Tukur Buratai yana faɗin cewa yaƙi da kungiyar Boko Haram da sauran ayyukan ta’adda zai iya kai wa shekaru 20 nan gaba.
Yanzu dai abin da ‘yan Najeriya suka sanya ido su gani shine gaskiyar kalaman na shugaban kasa wanda ya sha alwashin ganin bayan ayyukan ‘yan ta’adda a wannan shekarar ta 2021.