Tun a makon jiya aka kammala haska karshen zango na uku na shirin Labari na da ake haskawa a tashar Arewa24, wanda aka dunga tsumayen ci gaba da haske zango na gaba na shirin daya mamaye zukatan masu kallo.
An saba haska shirin duk ranar Litinin, to sai dai ana zargin cewar an sami matsala a tsakanin mahukunta tashar Arewa24 din da mamallaka shirin Labarina, mai dogon zango, har ake ganin ta iya yiwuwa ma a sauya tashar haska shirin zuwa wata tashar a maimakon tashar Arewa24 da aka saba haskawa.
Lallai dole akwai wani boyayen lamari kan dakatar da dora sabon shirin jiya Litinin, tare da fitarwar dena haska shirin a ƙuraren lokaci.
Hujjojin suna da tarin yawa, Mashiryin shirin da sauran masu ruwa da tsaki ciki harda mai rubutun ƙagaggen labarin Ibrahim Birniwa, basu bayyana zaa tafi hutu daga haska shirin ba sai jiya Litinin kuma ya rage saura Minti bai fi 20 a fara haska shirin ba suka sanar da cewar bazaa ci gaba da haska shirin ba a jiya.
Har ila yau sanarwa da Aminu Saira, ya fita ta bayyana cewar baza a ci gaba da haskawar ba kuma babu tabbataccen lokacin da suka bayyana na lokacin ci gaba da haska shirin sai dai sun cewa idan lokaci yayi zasu bayyana tashar da zaa ci gaba da haska shirin da kuma lokacin fara haska shi.
Ana zargin an sami dan rashin jituwa tsakanin tashar Arewa24 da masu ruwa da tsaki kan shirin Labarina, mai dogon zango wanda hakan ya saka dole aka dakatar da haska sabo, aka dauko tsohon tun daga farko aka saka saboda cece-kucen mutane.
Har ila yau wasu masu nazari sun zargi cewar kamar masu tashar AREWA24 sun fi amfana da tagomashin shirin a maimakon masu daukar shirin, hakan ya saka zaa koma kallon shirin a YouTube kawai a maimakon a Talabijin.
So watt