Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da ɓarkewar rikicin ƙabilanci a wani kauye na jihar.
Rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa mazauna garin Tinno da kabilar Chobo da ke karamar hukumar Lamorde.
Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a cikin rikicin.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa wani karamin saɓani aka samu bayan wani matashi ya kaɗe wani ɗan kabilar Chobo.
Daga bisani `yan uwansa suka far ma mai babur ɗin, inda shi ma wasu suka yi kokarin kare shi, kuma wasa-wasa rikici ya girma.