Ministan tsaro ya bukaci ƴan Najeriya su bar jin tsoron ƴan bindiga
Major General Magashi
Ministan tsaro Mejo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya bukaci ƴan Najeriya da su yi ta maza su tunkari ƴan bindigar da suka addabi ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana bayyana ƴan bindigar da suka sace mutane a makarantar sakandire ta kwana a Kagara a jihar Neja a matsayin matsorata.
Ya ce ƴan Najeriya na da alhakin tabbatar da cewa akwai matukar tsaro a inda suke. Ya ce haƙƙin kowa da kowa ne a yi taka-tsan-tsan don tabbatar da tsaro ba wai sojoji ba kaɗai.
Jaridar ta ruwaito Magashi da cewa “Bai kamata mu zama matsorata ba. Wani lokaci ƴan bindigar nan zuwa suke yi da harsasai uku kawai, da sun harba sai kowa ya gudu. A lokacin da muke matasa tsayawa muke yi mu fafata da ko wace irin barazana.
“Kamata ya yi mu tsaya mu tunkare su. Idan suka fahimci muna da karsashin kare kanmu, za su gudu,” a cewarsa.