Wani jigo a jam’iyyar APC, Farouq Aliyu, ya ce ba shugaba Buhari ba ne ya kamata ya amsa gayyatar majalisar tarayya ba dangane da matsalar tsaro a kasar nan.
Da ya ke zantawa da gidan talabijin din Channel ranar Laraba a Abuja, Aliyu ya bayyana cewa manyan hafsoshin tsaro ne ya kamata su bayyana a gaban yan majalisar don yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan irin matakan da su ke bi don kawo karshen matsalar tsaro.
“Idan zan ba wa shugaban kasa shawara, zan ce ma sa kar ya je. Zan ce masa ya tura hafsoshin tsaro don sai an fi samun bayanai muhimmai a wajen su,” a cewar sa.
“A matsayina na tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisa, ba na tunanin ya kamata shugaban ya je. Ba a irin wannan lokacin da komai ya yi tsauri ba, kasar ta na fama da matsaloli.
“Shugaban zai bayyana ne gaban majalisa don bayanin matakin da gwamnati ke dauka? “Zai je ne saboda mahawara? Ko shugaban majalisa ba zai ce ran shugaban kasa ko jam’iyyarsa bai baci ba da wannan gayyata”.
Da ya ke kare ikirarin sa kan cewa kar Buhari ya amsa gayyatar majalisar kan matsalar tsaro, tsohon shugaban marasa rinjayen ya ce shugaban kasar ba mai yawan magana bane.