Hon. Mudassir Ibrahim Zawachiki shine mamba mai wakiltar mazabar Kumbotso a Majalisar Dokokin Jihar Kano. A cikin wannan tattaunawar da Aminiya, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya yi gwagwarmaya daga sana’ar sayar da shayi har zuwa lokacin da ya zama dan majalisa.
Ku biyo mu:
Ko za ka iya gabatar mana da kan ka?
To ni dai suna na Hon. Mudassir Ibrahim Zawachiki, ni ne mamba mai wakiltar mazabar Kumbotso a Majalisar Dokokin Jihar Kano. Na yi karatu a Kwalejin Rumfa dake Kano daga bisani kuma na wuce zuwa Kwalejin Fasaha ta jihar Kano inda na karanci Aikin Jarida.
An zabe ni a matsayin Kansila mai wakiltar mazabar Panshekara kuma shugaban Kansiloli a wannan Karamar Hukumar ta Kumbotso.
Daga bisani kuma an zabe ni a matsayin dan Majalisa mai wakiltar Kumbotso karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019.
Kafin ka shiga siyasa, ko akwai wata gwagwarmayar sana’a da ka yi?
Alhamdulillah, tun ina dan karami, mahaifi na wanda dan kasuwa ne a kasuwar Singa dake Kano kuma yana sana’ar sayar da hatsi da sauran kayan abinci. To na kan bi shi kuma in koyi sana’a.
Daga baya kuma sha’anin rayuwa abubuwa suka canza sai na yanke shawarar neman mafita saboda ba zai yuwu mutum ya zauna haka kawai ba.
Daga nan ne na tsunduma sana’ar sayar da shayi, duk da haka kuma ina ci gaba da bin mahaifin nawa wurin sayo hatsin. A zahirin gaskiya ma kusan har da na zama dan majalisar na kan bi shi zuwa wasu jihohi kamar Taraba, Adamawa da Gombe domin sayo hatsi kamar Masara, Shinkafa da Gyada.
Mutane da dama za su yi mamakin ka taba sayar da shayi la’akari da matsayin da kake kai yanzu. Wanne darasi ka koya har ka yanke shawarar shiga sana’ar?
To Alhamdulillah, shi Allah a kullum ya kan duba zuciyar mutum in niyyar sa mai kyau ce. Ni gaskiya tun kuruciya ta ba abinda nake so kamar sana’a. A kullum tunani na bai wuce yadda zan juya kwandala ta koma Naira 10 ba.
Mahaifi na ya kan kai ni shago tun ina yaro, tun ban ma iya kirga kudi ba, mu kan sayi hatsin da ya kai kusan buhu 200 (a wancan lokacin), amma duk da haka ya kan ajiye ni a sahgon har sai da ta kai lokacin da sai dai kawai a turo min da kaya na tura masa kudi in su ka kare.
A rayuwa, duk a inda ka tsinci kan ka kawai ka gode wa Allah. Lokacin da abubuwa suka canza a harkokin sana’ar mahaifi na sai na yanke rungumar sana’ar shayi, tun a lokacin ma ina matakin karatun sakandire. Na kan hada sana’ar da zuwa makaranta a lokacin.
Amma babban ginshikin dai shine kada mutum ya raina kowacce irin sana’a. Ni abinda na yi amanna da shi shine ba na raina kowacce irin sana’a komai kankantar ta. Ko a lokacin da na shiga siyasa, wasu kawai sai su kalle ni su ce, “Sai Mai Shayi” ni kuma sai in yi dariya in amsa musu, saboda sana’a ta ce kuma ina alfahari da ita.
A duk cikin sa’o’i na mutum shida, wasu ma’aikatan gwamnati ne, wasu malaman makaranta, amma abin mamaki babu wanda ba ya zuwa wuri na aron kudi, duk albarkacin wannan sana’ar ta shayi. Hatta gidan da nake ciki a yanzu haka da sana’ar na gina shi.
A wancan lokacin, don kana ma’aikaci mai daukar N150,000 a wata zan iya ja da kai. Na kan iya yin cinikin N70,000 zuwa N100,000 a kullum. Ba na shayin yin kowacce irin hidima daga N1,000 har zuwa N100,000 a lokacin.
Na yi sa’a na sami wuri a fuskar jama’a kuma mutane na zuwa wuri na sosai, ana ciniki. Alhamdulillah, Allah ya albarkaci kasuwancin nawa sosai. Akwai yara da yawa a karkashi na. Ta kai lokacin da ko ban je rumfar ba yara na za su kula da komai saboda yaran nawa za su kula da duk abinda ya kamata.
Mutum nawa ne su ke aiki karkashin ka a lokacin?
Akwai yara shida a karkashi na a lokacin.
Shin har yanzu wurin yana nan kuwa la’akari da matsayin ka na yanzu?
Kwarai kuwa, har yanzu yana aiki. Ko ma kafin na bar wurin, uku daga cikin yaran da ke aiki a karkashi na sun bude wuraren su, amma har yanzu babbar rumfar tana nan tana aiki.
Akwai kani na da yanzu haka yake kula da wajen. Kuma Alhamdulilah yana ci gaba da kula da shi har ma ya kammala karatun NCE duk da wurin.
Ganin yadda yanzu Allah ya albarkaci sana’ar ka har ka kawo matsayin da ka ke kai yanzu, wanne sako ka ke da shi ga matasa?
Ina kira gare su da kada su sake su raina kowacce irin sana’a. Yawancin su suna da tunanin yin kudi a dare daya ba tare da yin sana’a ba. Ita sana’a kuma tana bukatar hakuri da juriya ta yadda za ka ci gaba da kula da kwastomomi da ma shi kan sa kasuwancin naka.
Matasa su daina kallon masu kudi kawai suna son zama kamar su ba tare da duba gwagwarmayar su ka sha ba. Ba ka san wahalar da mai kudi ya sha ba kafin ya tara su. Saboda haka dole sai mutum ya yi hakuri.
Akwai abubuwa biyu da na yi la’akari da su da ke zama kalubale ga matasan mu a yau; na farko idan suka fara sana’a yau, so suke gobe su yi kudi, na biyu kuma akwai masu kudi da yawa da ke son fara sana’a amma suna fargabar wanda za su dauka ya rike musu amana.
Yawancin matasan mu a yau sun gwammace su rika sayen manyan wayoyi da sutturu masu tsada, shi kuwa kasuwanci bai gaji wannan ba. Dole ka ware uwa ka ware riba kafin ka san nawa za ka kashe. Duk wanda ya ke kashe sama da abinda yake samu to tabbas kasuwancin sa babu inda zai je.
Amma idan mutum ya yi hakuri, da sannu sai ya kai ga inda ya ke mafarkin zuwa. Ya kamata matasan mu su yi koyi da irin su A.A. Rano. Na taba ji ana hira da shi ya ce har tallan manja ya taba yi da sauran sana’o’i. Yanzu kalli inda Allah ya kai shi. Mutum ba zai iya kaucewa abinda Allah ya tsara masa ba.
Ina kira ga matasa musamman na Kano su yi amfani da damar kasuwancin da take a garin kasancewar sa cibiyar kasuwanci ba a iya Najeriya kadai ba. Kusan ko ina a Kano yanzu kasuwa ne.
Mutum zai iya farawa da wata ‘yar karamar sana’a a cikin unguwar su, in ta bunkasa daga nan sai ya canza ya koma wacce yake hari, wata rana sai ka ga Allah ya sa albarka a ciki ta bunkasa. A kullum Allah ya kan duba kyawun niyyar mutum.
A matsayinka na ganau ba jiyau ba, ko akwai wani yunkuri da ka ke yi na tallafa wa matsa su ma su bi sahun ka?
Kusan kullum mu dama akidar siyasar mu kenan ta tallafa wa mutane. A kullum kuma muna tallafa musu su tsaya da kafafun su. Buri na shine har kullum in ga mutane na ci gaba, ina so in ga wani a inda na bari.
Amma babban jigon dai shine dole mutum ya bi hanyar da ta kamata ya kuma hada da hakuri. Yau ga ni a nan, gobe kuma wani ne a wurin. Ina fatan ganin duk wanda ya taka wata rawa wurin ci gaban mu shima an tallafa masa.