Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a ranar bikin tunawa da tsofaffin sojoji na shekarar 2021 da ya gudana a birnin tarayya Abuja, kamar yadda mai bashi shawara akan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya bayyana.
Shugaban kasa Buhari yace, ana yin wannan taron ne don tunatar da ‘yan Najeriya gudummawar da rundunar Soji ta bayar, da yadda jama’a za su yi kishin kasa da kuma kawo hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya, wanda yayi wahala matuka kafin ya kai wannan matakin.
Buhari ya kuma roki ‘yan Najeriya da su kiyaye yin abubuwan da za su kawo rabuwar kawuna tsakaninsu. Shugaban kasa ya kara da cewa, jami’an tsaro sun yi iyakar kokarinsu wurin kawo zaman lafiya arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya.
Wanda hakan ya taimakawa Najeriya musamman yankin Arewa domin yanzu haka arewa na cikin kwanciyar hankali sosai idan aka kwatanta da baya.
“kasarmu ta fuskanci kalubale iri-iri a harkar tsaro tun da Najeriya ta samu ‘yancin kanta.
“Wadannan kalubalen ya jawo tattalin arzikin Najeriya, ilimi, harkokin lafiya da na noma sun yi kasa.”Ina farin cikin yadda aka samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas da tsakiyan arewacin Najeriya.”