Guardiola ya taya kocin Bayern Munich murna da dukkanin yan wasanta saboda nasarar da ta kungiyar ta samu na lashe kufuna shida a kakar wasa daya.
Guardiola yace “ina alfahari, ina kuma taya murna ga kowa, musamman kocin kungiyar Hansi Flick],‘ saboda wannan abin mamakin.
“Amma ina so in ce wa Hansi cewa su ne na biyu a irin wananan bajintar na lashe kofuna shida a jere!
“Kafin ku, nine nayi irin wannan bajintar a kungiyar, Barcelona a 2009.
Guradiola ya kara da cewa yace watakila zai iya kira Messi domin kafa wani tarihin na lashe kufuna bakwai a kaka guda bakwai.