Sabon Kamfanin jirgin sama na United Nigeria ya fara tashi daga Legas zuwa Enugu da kuma zuwa Abuja a yau Juma’a.
Daman Shugaban Sadarwa na Kamfanin Mista Achilleus-Chud Uchegbu, ya bayyana a ranar Alhamis cewa jirjin zai fara tashi ayau Juma’a.
Uchegbu ya ce jirgin zai fara aiki ne a yau Juma’a bayan da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, wato NCAA ta bayar da Takardar shaidar fara tashin jirgin ta AOC, zuwa ga kamfanin jirgin na United Nigeria, bayan da kamfanin ya cika duk wasu ka’idoji da suka dace na fara aiki.