Dikko Shine Yayi Kokarin Gyara Ingantuwar Hanyoyin Shigar Kwastom
Kanwan Katsina, Alh. Bello An bayyana rasuwar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Late Abdullahi Inde Dikko, a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da ma kasa baki daya. Kanwan Katsina kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta shugabannin kauyuka da sauran masu rike da sarautun gargajiya, a ziyarar ta’aziya ga dangin mamacin a Katsina.
A cewar Alh. Bello, ya samu kaduwa da labarin rasuwar Abdullahi Dikko.
Ya bayyana cewa tsohon Kwanturolan na Kwastam din Janar din, shi ne tsohon shugaban nasa wanda ya yi aiki tare na kimanin shekaru talatin.
Mai rike da sarautar gargajiyar, ya ce Dikko ya kawo sauye-sauye da yawa a cikin aikin, musamman aikin komputa na ayyukan Kwastam, wanda ya inganta samar da kudaden shiga ga Gwamnatin Tarayya. Alh. Usman Bello, ya kara da cewa marigayin, a matsayinsa na shugaban Kwastam, ya samu gagarumar nasara a bangaren horaswa da sake horas da ma’aikatan hukumar, tare da inganta walwalar ma’aikatansa.
Kanwan Katsina, ya samu tarba daga dan uwan mamacin kuma Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Sagir Bature, da sauran ‘yan uwa. Ya yi addu’ar Allah ya jikan Abdullahi Dikko ya kuma roki Allah da ya baiwa iyalai juriyar jure rashin.