Masu ruwa da tsaki a jihar Neja sun zargi Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yaudaransu duk da dubunnan kuri’un da suka bashi a zaben 2015 da 2019, sai gashi ya watsa musu ƙasa a ido.
Dattawan sun bayyana cewa babu abinda Buhari ya tsinana musu tun lokacin da ya hau mulki. Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Minna a taron da karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, ya shirya.
Wadannan masu ruwa da tsakin sun hada da lyan majalisu, sarakunan gargajiya, kungiyoyin matasa, kungiyoyin mata, da malaman addini.
Duka sun bayyana ra’ayoyinsu kan irin kalubalen da jihar ke fuskanta. Sun bayyana yadda suke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rashin hanyoyi masu kyau, da rashin wutan lantarki.
Shugaban matasan jihar, Bello Sharif, ya ce shugaba Buhari ya yaudari jihar duk da irin goyon bayan da ya samu lokacin zabensa na farko da na biyu, amma daga baya yake hanasu romon demokradiyya.
“Muna fushi da Shugaba Buhari, muna son shi amma shi baya son mu. Ya yaudare mu da tashar Baro ba su aiki, titunan jihar sama da kilomita 2000 sun lalace da sauran su”.
“Shi yasa muke kira ga ministoci da ‘yan majalisu su kawo mana dauki, kuma idan basu yi haka ba, idan suka kira Matasan Neja ba zasu sauraresu ba.”
Babban Limamin Minna, Malam Ibrahim Fari, ya ce rashin tsaro da rashin wutan lantarki na daga cikin manyan matsalolin da jihar ke bukata. “Muna son AEDC ya kara mana wutan lantarki a jihar.
Ba zamu amince da wuta kasa da sa’a 20 a rana ba, idan ba zasu iya bamu ba, su fita daga jiharmu, ” ya bayyana.
Don Samun Ingantatun Labarai Kuziyarci Shafin Mu FACEBOOK & TWITTER