Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ƙaddamar da titin jirgin ƙasa da zai taso daga Kano ya ratsa Katsina da Jibiya ya tsaya a Maraɗi cikin jamhuriyar Nijar.
A bikin ƙaddamar da aikin titin, wanda shugaban ya halarta ta intanet, ya ce titin zai bi ta manyan cibiyoyin kasuwanci kamar Kazaure da Daura da Katsina da Maraɗi.
Buhari ya ce wannan aiki mai muhimmanci zai tabbatar da ci gaban kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar.
Haka kuma ya ce hakan zai inganta hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasashen biyu.
Kamfanin Messrs Mota-Engil Nigeria Limited ne ke aikin shimfida titin, kuma zai gina wata makarantar koyon kimiyyar sufuri da titin jirgin ƙasa.
Shugaba Buhari ya yi kira ga masu zuba jari su sa hannu don ganin an samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi.