Kasar Mauritius ta bayyana cewa gaba daya wadanda su ka kamu da cutar COVID-19 sun warke.
A halin yanzu babu wani mai fama da wannan cuta a cikin kasar Afrikar. Mauritius ta shiga cikin jerin kasashen da yanzu babu mai jinyar Coronavirus.
Daga lokacin da annobar ta barke zuwa yanzu, mutane kusan 70,000 su ka kamu a Afrika. Har a zuwa jiya 12 ga watan Mayu, 2020, Lesotho ce kawai kasar da COVID-19 ba ta ratsa ba a Afrika. Kasashen Eritrea, Seychelles da Mauritania su na da mai jinya daya.
Kasar ta Mauritius ta ce yanzu kowa ya warke daga cikin mutane 322 da su ka kamu da cutar kwanaki. Mummunar cuta ta yi sanadiyyar mutuwar mutanen kasar goma.
https://twitter.com/AfricaFactsZone/status/1260125753091461120?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1260125753091461120&ref_url=https%3A%2F%2Fhausa.legit.ng%2F1329433-yanzu-babu-wani-mutum-mai-cutar-covid-19-a-kasar-mauritius—jamiai.html
Wannan labari ya na nufin akwai wannan cuta a cikin kasashe 52 na nahiyar Afrika. Coronavirus ta kashe mutane kusan 2, 400 a kasashen Afrika a cikin watanni kusan biyar.
Ga wadanda ba su da labari, Mauritius karamar kasa ce cikin tsibiri zagaye da teku kusa da yankin kudu maso gabashin nahiyar. Akwai kimanin mutane miliyan 1.2 a kasar. A ranar 11 ga watan Mayu, aka shafe rana ta biyar a jere da ba a samu bullar COVID-19 ba.
Ko da babu wanda kwayar cutar ta harba, gwamnati ta ba ta bada damar fita ba tukuna. A farkon makon nan ne ma’aikatar kiwon lafiya ta Mauritius ta ce ta yi wa mutane har 73, 572 gwaji. Ana yi wa mutane gwajin PCR ne da na ‘Rapid Antigen’ a asibitocin kasar.
Gwamnati ce ta ke daukar nauyin kula da ‘yan kasar Mauritius, duk wani ainihin ‘dan kasar zai iya sayen magani a duk shagon da ya ga dama ba tare da biyan ko sisin kobo ba.