Wani aure mai shekaru takwas ya kare a tashin hankali da rashin dadi a yankin Zumbagwe da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.
Ana zargin Janet Ekpe mai shekaru 33 da saka wa mijinta guba a abinci bayan ta zarge sa da soyayya da babbar kawar ta. Ta zuba ido har ya mutu a gaban ta.
Bayan zargin Sunday Ekpe da soyayya da kawarta, ta zarge sa da kaurace mata amma yana gamsar da babbar kawar ta.
Janet ta tuna yadda suke ma’amala da mijin ta da kuma gamsuwar da take samu tun bayan da suka yi aure, amma kwatsam sai ya juya mata baya, jaridar The Nation ta wallafa.
Ta ce ta gaji da bai wa mijin ta uzirin da ya ki karewa. Ta gaji da zaunar da shi don son sanin inda ta rage shi don tana yawan tunawa da lokutan da suke zama lafiya cike da soyayya.
Hankula sun fara tashi bayan da Janet ta gano mijin ta ya fada soyayyar babbar kawar ta kuma suna cin amanar ta.
Ta gano cewa hankalin sa ya dauke zuwa kawarta don ba shi da lokacinta kwata-kwata.
Ta yi tunanin cewa hanya daya da za ta bi don maganin halin da take ciki shine kashe Ekpe ta yadda duk wani takaicin rayuwa zai wuce mata.
Ba ta tsaya a kashe Ekpe kadai ba, ta cire mazakutar sa ta yadda ko a wata duniyar ba zai yi ma’amala da wata macen ba.
A kalaman Janet, ta ce sai a shekaru uku da suka gabata ne ta gano cewa mijinta na soyayya da babbar kawarta kuma yana matukar gamsar da ita.
Ta ce, ” Shekaru takwas kenan da aurenmu da shi. Ya saba gamsar da ni ba kadan ba. A wurinsa na saba da kwanciya sosai don a madafi, dakin bacci, bandaki da duk inda muka so muna jima’i.
Akwai ranakun da yake fasa zuwa aiki don kawai yana bukata ta. Baya gajiya ko kadan. Muna iya yi sau hudu da safe kuma mu sake bayan ya tashi bacci.
“Ya fara janye jikin shi ne a lokacin da muka haifa yara biyu. Zatona bayan na yaye yaron da nake goyo zai dawo amma sai na ji shiru.
“Da na tunkare sa da zancen sai ya ce shi ya gaji da kwanciyar auren idan ina bukata zan iya nemo wa a waje. Na kai karar sa coci amma bai sauya hali ba. Iyayensa da duk wanda ya isa ya yi masa magana amma shiru.”
Matar ta bayyana cewa daga bisani ta gano mijinta na tare da babbar kawar ta mai suna Hellen. Bayan ta tunkare sa sai ya ki saurarar ta.
Hakan kuwa ya harzuka ta har ta bashi guba sannan ta datse masa mazakuta saboda cin amana.