Wani alƙali a jihar Pennsylvania ta Amurka, ya yi watsi da ƙarar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Donald Trump ya kai, inda ya buƙaci a soke miliyoyin ƙuri’un da aka jefa ta hanyar akwatin gidan waya a yayin zaɓen ƙasar.
Alƙalin kotun, Mathew Brann, ya bayyan cewa ƙorafin da aka gabatar na zargin saɓa ƙa’idojin zaɓe bai da wani tushe.
Watsi da ƙarar da alƙalin ya yi za ta buɗe hanya domin tabbatar da Joe Biden a mako mai zuwa a matsayin wanda ya lashe jihar Pennsylvania – inda yake gaba da kusan ƙuri’u 80,000.
Wannan shi ne duka mafi ƙarfi na baya-bayan nan da Biden ɗin ya yi wa Trump a zaɓen ƙasar da Trump ɗin ya ƙi amincewa da sahihancinsa.