Support Daily Episode Journalism DONATE

‘Ba za a kammala titin Abuja zuwa Kano a zamanin Buhari ba’

‘Ba za a kammala titin Abuja zuwa Kano a zamanin Buhari ba’

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta fito fili ta bayyana cewa sai nan da shekarar 2025 za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kano da aka fara a 2018.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Kaduna, na wani babban ayari na gwamnatin tarayya.

Tawagar gwamnatin tarayyar ta ziyarci aikin da ake yi tsakanin Kaduna zuwa Kano inda ta ce ta gamsu da yadda ake gudanar da aikin, duk kuwa da cewa wasu al’ummar ƙasar na ƙorafi kan yadda wannan aiki ke tafiyar hawainiya.

Sai dai ra’ayin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sha bamban da na ministan ayyukan inda ya ce “za’a kammala aikin cikin wannan lokaci da shugaba Buhari ke jagorantar Najeriya”.

DAILY EPISODE

ZIYARCI SHAFIKANMU NA FACEBOOK & TWITTER 

Support Independent Journalism

We appeal to you to donate and support our journalism. The impact of our investigations has given hope to the vulnerable, held power accountable, and become a voice for the oppressed.
Be part of the accountability journey.

CATEGORIES

COMMENTS

Wordpress (0)
Disqus ( )