Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta amince jama’a su yi jam’in Sallar Idi a “masallatan Juma’a amma ba sai an fita filin Idi ba” saboda annobar korona.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamiti mai bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin Musulunci ya fitar ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwar da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta fitar, inda kwamitinta na fatawa ya ce “bai kamata a yi jam’in sallar ba kuma kowa ya yi ta a gidansa”.
Sai dai ko a sanarwa ta farko, fadar sarkin ta ce idan ya zama dole sai an yi jam’i – musamman a jihohin da aka bayar da dama – to a yi sallolin a masallatan cikin unguwanni.
Amma a sanarwa ta biyu fadar ta ce: “An umarci dukkanin iyayen ƙasa da hakimai da limaman Juma’a da su gabatar da Sallar Idi a masallatansu na Juma’a a garuruwansu ba tare da an fita filin Idi ba.”
Ta ƙara da cewa: “Haka kuma an hana mata da ƙananan yara zuwa Sallar Idin bana, sannan babu dukkan bukukuwa da tarukan al’adun gargajiya da gaisuwar sallah.”
Daga ƙarshe fadar ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da addu’o’in neman Allah ya kawo ƙarshen annobar.
Da ma dai tuni wasu gwamnonin jihohi suka bai wa jama’arsu damar ci gaba da gudanar da sallar Juma’a da kuma yin Sallar Idin ta bana.
Sai dai gwamnatin tarayyar Najeriya na ƙorafi kan sassauta dokokin kulle da gwamnonin ke yi a jihohinsu , inda ta ce “muna tufka jihohi na warwarewa” a yaƙin da ake yi da annobar korona a ƙasar.
Kazalika shi ma Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya shawarci gwamnonin da ke sassauta dokar kulle su yi taka-tsan-tsan .