Wani dalibin SS1 da aka ambata da suna Usamatu Aminu Male, ya bayyana jimillar dalibai dari biyar da ashirin (520) da aka sace a makarantar sakandaren gwamnati ta kankara.
Ku tuna cewa a yammacin ranar Juma’a wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba anma ana zaton cewa masu satar mutane ne, wadanda suka sace’ yan makaranta a karamar hukumar kankara da ke jihar katsina.
Usamatu Aminu Male wanda ya zanta da wakilin jaridar Daily Episode, ya ce ‘yan fashin sun tilasta musu yin tafiya na tsawon kilomita a cikin daji ba tare da sun huta ba.
Bayan tsawon awanni suna tafiya, wani shugaban gungun ya nemi su tsaya su kirga yaran , ‘yan bindingan sunka hada su waje guda, sai suka fadawa maigidan cewa daliban su 520 ne bayan kirgawa.
Sun ci gaba da doguwar tafiya zuwa inda ba a san inda suke ba, mafi yawan daliban sun fara kuka da korafin yunwa da gajiya, sun ce ba za su iya tafiya ba kuma, daya daga cikin ‘yan bindigan ya yi barazanar kashe duk wanda ya yi kokarin tsayawa, duk suka yi biyayya suka ci gaba. .
Daya daga cikin daliban yayi kokarin gudu amma daga baya yan bindigan suka kashe shi, Usamatu yace yayi sa’ar boyewa lokacin da suka tsaya a wani kogi da aka umartar daliban su sha ruwa.
Nan da nan na yi sauri na dawo wani kauye kusa da inda ya ga wani mutum yana barci a cikin masallaci ya nemi taimakonsa.
Daga baya mutumin ya dauke shi zuwa gidansa inda yake ba Usamatu shawarar kar ya bayyana wa kowa saboda ‘yan bindigan suna da masu basu bayanai a kauyen.
A safiyar jiya ne usamatu ya dawo bayan mutumin ya biya N250 ga wani dan acaba inda aka dawo dashi kankara kuma ya hade da yan uwansa.
Daga baya an mika Usmatu ga jami’an tsaro don kulada lafiyarsa da kuma ci gaba da bincike.