A ranar 9 ga watan Disambar kowace shekara ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin wayar da kai kan illolin cin hanci da rashawa da kuma yaƙi da cin hancin.
Najeriya na daga cikin ƙasashen da cin hanci da rashawa ya kassara, inda ake zargin cewa cin hancin ne ya sa matsalolin da ke faruwa a ƙasar ke ƙara ta’azzara.
Tun a lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara yaƙin neman zaɓe, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da shugaban ya fi mayar da hankali a kai shi ne yaƙi da cin hanci.
Shugaban dai ya yi alƙawarin kawar da cin hanci a ƙasar da kuma hukunta masu laifuka da ke da alaƙa da cin hancin. Jama’a da dama dai na ganin cewa an samu ci gaba a ɓangaren yaƙi da cin hanci a ƙasar, sai dai wasu na ganin cewa ci gaban irin na mai haƙar rijiya ne.
Shin kwaliyya na biyan kuɗin sabulu?
Kan wannan rana ta musamman, BBC ta tuntuɓi babban daraktan cibiyar wayar da kan al’umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci (CAJA), wato Kabiru Sa’idu Dakata, domin jin ta bakinsa inda ya shaida mana cewa babu abin da ya sauya a Najeriya kan batun cin hanci sai ma ƙaruwa.
Ya ce babban ƙalubale ko kuma ci baya da aka samu kan cin hanci da rashawa a Najeriya shi ne “zargin da ake yi wa tsohon shugaban hukumar EFCC a ƙasar kan cewa shi ma limami ne wurin cin hanci”.
Kabiru Dakata ya bayyana cewa babu wani ci gaba da aka samu sakamakon komai ya koma baya tun da shi ma shugaban hukumar EFCC ana zarginsa.
“Babu wani ci gaba da aka samu, an ɓata shekaru ne kawai a iska, an ƙara dasashe karsashin da ake da shi na fatan cewa za a iya yaƙi da cin hanci da rashawan nan, a lokacin Buhari ne fa ‘yan ƙasar ke cewa mun yi saranda ƙasar nan Allah ne zai gyara ta, wanda kafin zuwanshi an yi tunanin yadda ake nunawa za a yi.
“A wancan lokacin akwai fata za a iya magance yaƙi da cin hanci amma yanzu an yi saranda,” in ji Malam Kabiru.
Kallon da duniya ke yi wa Najeriya kan cin hanci
A shekarar 2018 rahoton Labarai da Rahotanni na Amurka watoU.S. News and World Report ya sanya Najeriya a ta ɗaya a jerin ƙasashen da aka fi cin hanci a duniya.
Amma a shekarar 2020 da muke ciki cibiyar da ke nazari kan yawan al’fummar duniya ta sanya Najeriya ta 26 cikin ƙasashen da cin hanci ya fi ƙamari a duniya.
Mece ce mafita?
Dangane da shawo kan matsaloli na yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, Kabiru Dakata ya bayar da wasu shawarwari da a ganinsa idan aka yi amfani da su, za a samu sauƙi.
Abu na farko da ya bayyana shi ne dawo da martabar hukumar EFCC a idon jama’a. Ya bayyana cewa mutuncin hukumar ko kuma darajarta ta ragu a idanun al’umma wanda hakan zai sa masu aikata laifi irin na cin hanci ba lallai su ji tsoron aikata laifin ba ganin cewa ana zargin tsoihon hugaban hukumar da cin hanci.
Ya kuma ƙara bayar da shawara da a dakatar da ‘yan sanda daga jagorancin hukumar a yanzu sakamakon kusan shugabannin hukumar har hudu babu wanda aka kwashe lafiya da su a ƙarshe.
Ya kuma bayyana cewa babban abin da ya kamata shugabanni su yi idan ana so a samu sauƙin cin hanci da rashawa shi ne adalci.
“Abin da yake na mutane ne, a rinƙa yi musu abin su, abubuwan da suka shafi ayyukan mazaɓu da kasafin kuɗi ya kasance al’umma biliyoyin nairan da suke ji ba wai a rediyo ne kaɗai ba, ya kamata su rinƙa gani a ƙwaryarsu, a titunansu da yanayin tsaronsu,” in ji shi.
Ya kuma ce ya kamata adalcin ya shafi yadda ake kashe kuɗin al’umma da kuma samar da ayyukan yi ta yadda ‘yan ƙasar sun rinƙa samun ayyukan yi bisa cancanta.