Daya daga cikin dalilan da suka sanya ‘yan Najeriya tururuwa wajen goyan bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari a zaben 2015 shi ne matsalar tsaro, sakamakon rikicin Boko Haram wanda ke ci gaba da hallaka jama’a musamman a jihohin arewa maso gabashin kasar har zuwa arewa maso kudu da tsakiyar kasar.
usa Yar’Adua, ta yi kamari ne lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan, inda mayakan kungiyar suka zafafa hare-hare kan tashoshin ‘yan sanda da Masallatai da Mujami’u da kasuwanni da makarantu da duk wani wuri da ake taron jama’a.
Daga harin bindiga, rikicin ya zafafa zuwa tada bama-bamai, abin da ya yi sanadiyar hallaka dimbin rayuka, ya kuma hana wasu jama’a zuwa wuraren ibadu da kasuwanni, yayin da iyaye ke fargabar tura ‘yayansu zuwa makarantu.
Boko Haram ta zafafa wadannan hare-hare zuwa jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da Adamawa da Plateau da ma babban birnin Tarayya Abuja, inda aka tada bam wurin taron kasa da shugaba Jonathan ke halarta, bayan munanan hare-hare irin wadanda aka kai Masallachin Fadar Sarkin Kano da Madalla da Nyanya da ke Abuja da Kasuwar Jos da Kasuwar Potiskum da Makarantar Buni Yadi da Chibok da ma wanda aka kai wa shi kansa Janar Buhari a Kaduna amma ya tsallake rijiya da baya.
Jam’iyyar adawa ta APC ta yi amfani da wannan tashin hankali wajen yakin neman zabenta a shekarar 2014, inda ta gabatar da Janar Buhari a matsayin dan takarar da zai sharewa al’ummar Najeriya hawaye, kuma masu zabe sun ba shi goyan bayan da ake bukata wajen samun nasara da kuma kada shugaba Jonathan mai ci da kuma Jam’iyyarsa ta PDP da ta kwashe shekaru 16 a karagar mulki.
A watanni farko na wannan gwamnati, an samu gagarumar nasara wajen kwato wasu yankuna daga hannun kungiyar Boko Haram musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda a karon farko aka ga shugaban rundunar sojin kasa Janar Yusuf Tukur Buratai a fagen daga yana fafatawa tare da dakarunsa, abin da ba a taba gani ba, matakin da ya karfafawa dakarun gwuiwar ci gaba da aiki.
Rundunonin tsaron sun yi asarar jami’ansu da dama cikinsu har da kwamandodi a wannan yakin, amma hakan bai hana su sadaukar da rayukansu ba.
Duk da asarar rayukan mutane sama da 36,000 sakamakon wannan rikici da kuma raba mutane akalla sama da miliyan biyu da gidajensu kamar yadda akaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna, wannan gwamnati ta yi nasarar dakile hare-haren kungiyar da kuma mayar da mutane garuruwansu na assali.
Sai dai yanzu haka wadanann nasarorin da aka samu na ci gaba da dakushewa sakamakon sake dawowar hare-haren da ake samu, musamman na makon jiya, inda mayakan suka yanka manoma 78, abin da ya tada hankalin al’ummar kasar baki daya.
Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya tabbatar da kisan a faifan bidiyon da ya fitar, wanda ya ce na ramako ne sakamakon kashe mabiyansa da kuma mika wani ga jami’an tsaro.
Wannan kazamin hari da kuma wasu matsalolin tsaron da suka adabbi yankin arewacin Najeriya, musamman na ‘yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane domin karbar diyya a yankin arewa maso yammacin Najeriya da arewa ta tsakiya sun jefa matukar shakku kan ko shugaban kasa Buhari yana da masaniyar halin da kasar ke ciki kuwa, ganin a watannin da suka gabata baya iya barin fadarsa domin tafiye-tafiye cikin kasar domin ganawa da jama’a da wasu shugabanni kamar yadda ya saba yi a baya.
Daga Jihar Sokoto zuwa Zamafara da Niger da Nasarawa da Plateau da Benue da Taraba da Adamawa da Bauchi da ita kan ta Abuja, kashe mutanen da yan bindiga keyi ya zama ruwan dare, yayin da garkuwa da mutane domin karbar diyya ya zama wani abin yau da kullum.
Yayin da shugabanni da masu mulki ke amfani da jiragen sama da na kasa wajen tafiye-tafiye a yankin arewacin kasar domin kauce wa irin wadannan bata-gari, an bar talakawa da rungumar kaddara wajen daukar makomarsu a hannu daga wadannan bata-gari da ke kashe su ba tare da kakkautawa ba, ko kuma kama su kamar kaji ana karbar diyya, wanda wani lokaci ke kai ga karbar kudin fansa da kuma hallaka su baki daya.
Daga ‘yan Majalisa zuwa masu rike da sarautun gargajiya zuwa malaman addinai da dalibai da malaman jami’a da likitoci har ma da jami’an tsaro, babu wanda bai taba fadawa hannun wadannan mutane masu garkuwa da mutane ba, kuma akasari sai da suka biya diyya kafin kubutar da rayukansu, ga wadanda suka tsira kenan.
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta yi rahoto na musamman kan mutane sama da 1,500 da aka kama daga watan Janairu zuwa Nuwamban wannan shekara kuma sai da suka biya miliyoyin Naira kafin kubutar da kansu.
A jihohi kuwa kamar Zamfara da Sokoto da Katsina da Adamawa an samu rahotannin da ke nuna cewar wadannan ‘yan bindiga kan aike da sako ga garuruwa a ba su kudi ko kuma su kaiwa garuruwan hari, yayin da kuma suke sanya haraji ga manoma kafin su yi noma ko girbi duk da rahotanni sasantawar da aka yi tsakaninsu da gwamnati a jihohin Zamfara da Katsina wadanda daga bisani suka rushe.
Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Saad Abubakar a makon jiya ya fito karara inda ya bayyana irin tabarbarewar da yankin arewacin kasar ya samu kansa, inda yake cewa yau har gida gida ‘yan bindiga ke bi suna kama mutane abin da ya mayar da yankin mafi wahalar rayuwa a Najeriya, korafin da ya yi daidai da na kungiyar ‘yan arewacin kasar da ake kira ACF.
Ita ma Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bayyana cewar, yau ran Bil’adama ba shi da tasiri a karkashin mulkin shugaba Buhari saboda ganin yadda tsaro ya tabarbare a yankin baki daya.
Majalisar Wakilai da ta Dattawa duk sun koka dangane da wannan matsala a wannan mako, inda suka bukaci garambawul ga bangarorin tsaron baki daya, kuma a wannan karon har tauna tsakuwa suka yi, ganin yadda fadar shugaban kasar kan yi kunnen uwar shegu da kudirorin da suke yi dangane da halin da kasa ke ciki.
Sau tari gwamnatin kan kare matakan da take dauka da kuma bayyana irin nasarorin da suke samu ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa ko Ministan Yada Labarai ko kuma Ministan ‘Yan Sanda.
Amma shi kuwa talakan Najeriya tambayar da yake yi ita ce, anya Buharin da suka sani ya san halin da suke ciki kuwa, ganin yadda ko magana ba ya yi dangane da irin ukubar da suka shiga da kuma yadda ake zub da jini ba tare da kakkautawa ba.
Yau tafiya daga gari zuwa wani gari a yankin arewacin Najeriya ya zama tashin hankali, ko kuma shiga da alwalarka, saboda fargaba da tashin hankalin da ake fuskanta, yayin da wasu manoma da dama suka guje wa gonakinsu, wasu kuma da suka yi noman sun kasa zuwa girbi, matsalar da ke haifar da barazanar samun abincin da jama’a za su ci, yayin da mazauna gida ma ba su tsira ba, kamar yadda wasu jama’ar jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina ke bayyana cewar a daji suke kwana domin tsira da rayukansu.
Lura da irin wannan mawuyacin halin da kasar ta shiga da kuma yadda ake zub da jini, ya sa jama’ar kasar da dama ke tambayar ko ina makomar yankin arewacin kasar da ke rike da shugabanci da kuma jagorancin rundinonin tsaro? Shin wa zai ceto yankin da kuma kare rayukan jama’ar da ke ciki ? Ina mafita take dangane da wannan mummunar yanayin da ya jefa arewacin Najeriya cikin tashin hankalin da ba a taba gani ba, ya kuma mayar da shi baya a kowanne bangare? Shin Buharin ne kuwa?