Ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar yanar gizo, Dr Isa Ali Pantami ya ce zai miƙa saƙwannin jama’ar Arewa ga Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi na manoma 43 a jihar Borno.
A ranar asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, dake ƙaramar hukumar Jere, jihar Borno, sun bi manoma har gonakinsu sun yi musu yankan rago.
Sheik Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na sadarwarsa a manhajar Tuwita bayan wani mai amfani da shafin ya roƙe shi da yin hakan.
Wanda yayi roƙon mai suna Boss Mustapha@__yellows) ya rubuta kamar haka. Don Allah don Annabi ka samu ka yi ma shugaban ƙasa magana. Mutum arba’in da uku (43), ko a fim aka kashe wannan adadi lokaci daya, abun zai bada tsoro.
“Don Allah a taimaka a yi wani abun a kai, abun ya fara yawa #ZabarmariMassacre”.
Shi kuma Pantami sai ya mayar masa da martani cikin harshen turanci kamar haka. “Muna ta yin hakan, kuma zamu cigaba da yin hakan In sha Allah. “Shi ma zan yi masa magana kamar yadda nayi magana da gwamna Zulum ɗazun nan. “Allah ya jiƙansu, ya kuma kawo mana ƙarshen wannan bala’in”.
Arewacin Najeriya dai na fama da matsanancin matsalar rashin tsaro da ta haɗar da Boko Haram, ƴan bindiga, ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane.
Rahotanni daga ƙididdigar baya bayan nan sun nuna cewa an yi garkuwa da fiye da mutane 1,500 a arewacin Najeriya baya ga biyan ɗimbin kuɗaɗen fansa.
Kazalika, rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 36,000 rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukansu tun daga shekarar 2009, da ƙungiyar ta ɓulla, zuwa yanzu.
Kazalika ayyukan ƙungiyar sun tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin muhallansu, inda ƴan Najeriya 240,000 suka yi gudun hijira zuwa maƙwabtan ƙasashe.
ZIYARCI SHAFUKANMU NA FACEBOOK & TWITTER