Rikicin kabilanci ya barke tsakanin Fulani da Tibabe a Nassarawa, 5 sun mutu
Tirkashi:Ankashe mutane Biyar A Jahar Nasarawa
Akalla mutane biyar ne suka mutu sakamakon wata sabuwar rikici da ya barke tsakanin kabilun Fulani da Tibie a jahar Nassarawa.
Daily Trust ta ruwaito baya ga kisan kai da aka yi, mutane da dama sun jikkata a rikicin daya barke a lardin Kadarko, cikin karamar hukumar Keana, a kan iyakar Nassarawa da Benuwe.
Wani dan kabilar ya bayyana cewa rikicin ya faro ne bayan wani dan Fulani ya gamu da wata mata yar tibi a gona, inda ya mata dukan kawo wuka haka nan ba tare da wani laifi ba.
Ihun da matar ta yi na neman agaji ya sa wani dan tibi dake noma a gonarsa ya yi kokarin kai mata dauki, amma bafulatanin ya fi karfinsa, kuma yay a sassare shi a kai da hannu.
“Ganin haka yasa matasan kabilar Tibi suka harzuka, suka tafi daukan fansa inda suka afka ma wasu yan Fulani da suka yi gudun hijira daga gari Udei na jahar Benuwe. “Su ma yan Fulani sai suka sake yin kwamba, suka kai hari a ranar Asabar, inda suka kashe mata biyu a wata gona da misalin karfe 9 na safe.” Inji shi.
Amma wani jami’in kungiyar Miyetti Allah da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa matasan kabilar Tibi sun kashe musu Fulani guda uku kwanaki uku da suka wuce a Yelwata.
Shugaban karamar hukumar Keana, Adamu Adi Giza ya tabbatar da hare haren tsakanin kabilun biyu, kuma ya bada tabbacin hukumar na yin duk mai yiwuwa don shawo kan lamarin.
“Na samu labarin an kashe Fulani guda biyu, haka zalika an kashe mata yan kabilar Tibi guda biyu, amma har yanzu ban samu cikkaken rahoton lamarin ba.” Inji shi.
i love this outstanding post