Zuwa ga Alummar Jahar Katsina, Talakawa na Birni dana karkara, Malamai, Limamai da Masarautar Katsina a cikin Shirin Barkada Warhaka na Gidan Radio Freedom Kaduna.
Kai Tsaye Mahadi Ya Bayyana cewa Yana mika Sakon shine ga Al’ummar Jahar Katsina Milyan Bakwai da Dubu Dari Takwas da Talatin da Daya da Dari Ukku (7,831,300)
Mahadi ya Bayyana cewa Daga Shekarar Dubu Biyu da Sha Biyar zuwa Dubu Biyu da Sha Tara Gwamnatin Jahar Katsina ta Kashe Naira Milyan Dubu Ashirin da Hudu, wato Bilyan Ashirin da Hudu (24,000,000,000.00) daga Asusun kula da Tsaro na Jahar Katsina (security vote).
Yayi Bayani Dalla Dalla yadda aka Wawushe Kudin da Kuma Asusunan da aka tura Kudaden, ya Bayyana cewa Karshen watan Biyar na Shekarar Dubu Biyu da Sha Takwas an ba S.A Political kudi Naira Milyan Dari Biyar domin zuwa Conversation a Abuja.
Haka nan ya Bayyana wasu Asusunan Banki har Guda Ukku da ya Bayyana cewa an baiwa kowane daga cikin su Naira Milyan Dari da Ashirin da Biyar.
Jami’an Tsaron Yansanda:-
Kazalika An ware wasu Kudade domin bada Tsaro a wutar Lambar Rimi, zunzutun Kudi Naira Milyan Dari Shidda da Tamanin da Hudu da Dubu Dari Ukku da Talatin da Shidda da Dari Shidda domin Yansanda Kwara Goma Tsawon Shekaru Hudu.
Limamai da Malamai:-
Bayanan sun nuna cewa a cikin Shekarar Dubu Biyu da Sha Biyar Gwamnatin da ta gabata taba Malamai kudi Naira Dubu Dari Takwas da Hamsin domin sayen Riguna, a Shekarar Dubu Biyu da Sha Shidda itama wannan Gwamnatin ta Biya su irin wadannan kudin sai dai Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai abun ya Chanza domin an ware Kudi a Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai Naira Milyan Dari Hudu da Chas’in da Takwas da Dubu Dari da Ashirin da Biyar da Naira Dari Biyu da Hamsin da Takwas domin sayen Riguna ga Limaman na Katsina, a Shekarar Dubu Biyu da Sha Takwas kuma an ware Naira Milyan Talatin da Shidda, sai Kuma aka ware Naira Milyan Ashirin da Biyar domin Kungiyar Izala ta Kaduna da Kuma Naira Dubu Dari Biyar domin Bangaren Izalar Jos.
Sayen Wayoyin Salular:-
Sannan Kuma an sayi Wayoyin Salula Sau Ukku Kamar haka:
i- Naira Milyan Dari da Biyar Domin Membobin Majalisar Tsaro na Jahar nan
ii- Naira Milyan Dari Ukku da Goma Sha Hudu Domin Chairmomin Kananan Hukumomin Jahar nan na rukon Kwarya
iii- Naira Milyan Dari da Sha Hudu Domin Yan Majalisar Jahar nan
Masarautar Katsina:-
Mahadi ya Bayyana cewa An ware ma Masarautar Katsina Naira Milyan Dari da Sittin da Biyar domin Ran Gadi zuwa Dajin Rugu.
Haka nan an sake ware wasu kudin Naira Milyan Talatin da Biyar domin yin Taron Tsaro duk da sunan Masarautar Katsina.
Mahadi ya Bayyana cewa a cikin Watan Sha Daya na Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai wani Babban Jami’an tsaro yazo Jahar Katsina an ware kudi Naira Milyan Dari Biyu da Hamsin an bashi kyauta.
Haka nan an ware Naira Milyan Dari da Saba’in an Baiwa Jami’an tsaron Gidan Gwamnatin da sunan welfare.
Mahadi ya Bayyana cewa zuwa Karshen watan da yagaba Tarin Maaikatan da sukayi Ritaya a fadin Jahar nan zasu kai Mutane Dubu Ashirin da Biyar kuma suna bin bashin Fanshon su na yawan Naira Bilyan Goma Sha Biyu, ya Kara da Cewa Yanzu Jahar Katsina tana fama da Bashin Naira Bilyan Chas’in da Shidda akan ta.
Mahadi yache duk Abubuwan da ya fadi yanada Hujjoji akansu Idan an tsakureshi zai bada, yama kara da Cewa Akwai Badakalar kashe Kudaden da akayi da bai Bayyana ba Kimanin Dari da Goma Sha Takwas wadanda bai Bayyana ba sai zuwa nan gaba idan Lokachin yin hakan yayi, ya kuma che Idan ya Bayyana su wannan da ya Bayyana kamar wasan Yara ne.