Malam Nasir Ahmad El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna, ya shafe ranakun Juma’a da Asabar a kan iyakar Kaduna da Kano domin tabbatar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.
Da ma El-Rufai ya lashi takobin cewa babu wanda zai shigar masa jiha daga Kano, biyo bayan matakin da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ɗauka na ci gaba da yin sallar Juma’a da kuma ta Idi a Kanon.
Malam Nasir @elrufai is at the Kaduna-Kano boundary for the second consecutive day to supervise the enforcement of the prohibition of interstate travel. pic.twitter.com/eouObEh8mT
— Governor of Kaduna (@GovKaduna) May 23, 2020
Kawo yanzu, a hukumance gwamnatin jihar Kaduna ba ta bayyana adadin ababen hawan da gwamnan ya tare ba ko ya mayar da su inda suka fito a zaman da ya yi a kan iyakar.
Sai dai a wasu hotuna da ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga hotunan gwamnan ya na tattaunawa da direbobin motoci sanan akwai alamun cinkosson ababen hawa a iyakar jihohin biyu
‘Cacar baki saboda almajirai’
Kafin yanzu, Elrufa’i ya yi ta nanata cewa mafi yawancin masu cutar korona a jiharsa almajiran da Gwamna Ganduje ya mayar da su ne daga Kano, abin da ya sa ake ganin kamar hakan ya jawo zaman doya da manja tsakanin shugabannin biyu.
Wannan magana ba ta yi wa Ganduje daɗi ba, inda ya mayar da martani a wata sanarwa cewa: “Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka mu ma ake dawo mana da almajirai ‘yan asalin jihar Kano daga wasu jihohin.”
Ya ƙara da cewa: “Don ba ma yin surutu a kan batun, ba yana nufin dukkansu lafiyarsu kalau ake kawo mana ba, ko ba sa dauke da COVID-19.”
A jihar Kano hukumomi sun tabbatar da mutum 896 ne ke dauke da cutar korona sanann wasu 36 kuma sun rasu, ita ce kuma kan gaba a yawan adadin a jihohin arewacin Najeriya baki ɗaya, kuma ta biyu a ƙasar bayan Jihar Legas.
Ita kuwa Kaduna ta na da mutum 189 da suka harbu da cutar korona ya zuwa safiyar Litinin, a cewar hukumar NCDC, yayin da biyar suka mutu da kuma 116 da suka warke.